‘Yan sanda sun buɗe sakatariyar karamar hukumar Filato

1
340

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, Okoro Julius-Alawari, ya bayar da umarnin a buɗe dukkanin sakatariyar ƙananan hukumomi 17 na jihar, watanni biyu bayan rufe su.

Idan dai ba a manta ba a farkon watan Yuli ne rundunar ‘yan sandan jihar ta rufe ƙofar shiga Sakatariyar, biyo bayan korar shugabannin ƙananan hukumomi da kansilolin da Gwamna Caleb Mutfwang ya yi.

Matakin da gwamnan ya ɗauka ya janyo cece-kuce da tada hankali, lamarin da ya kai ga rufe sakatariyar majalisar da ‘yan sanda suka yi.

Da yake bada umarnin buɗe ofisoshin ta wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Alfred Alabo ya fitar, CP ya ce an ɗauki matakin ne domin a ƙyale zaɓaɓɓun shugabanni na dimokuraɗiyya da kansilolinsu don gudanar da ayyukan gudanarwa yadda ya kamata.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a jihar Filato sun kashe sabbin ma’aurata

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A wani ɓangare na ƙoƙarin tabbatar da gudanar da ingantaccen aiki na sakatarorin ƙananan hukumomi 17 na jihar, rundunar ‘yan sanda ta yi nazari sosai kan lamarin tare da umurci kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato da ya buɗe dukkan ofisoshin ƙananan hukumomin jihar.

Shuwagabannin kansiloli da na kansilolin su baiwa dukkan zababbun shugabanni da kansiloli damar shiga ofisoshinsu daban-daban ba tare da wani shamaki ba, har sai an kammala shari’arsu a kotu.”

Sanarwar ta kuma bayyana cewa a yanzu haka shugabannin 17 a faɗin jihar za su samu damar shiga ofisoshinsu sannan su koma bakin aiki a ranar Litinin 28 ga watan Agusta.

1 COMMENT

Leave a Reply