Ambaliyar ruwa ya kashe mutane 32 a Nijar

1
273

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙasar Nijar mai fama da rikicin juyin mulki, na fama da matsanancin ambaliyar ruwa.
Kamfanin dillancin labaran Nijar (ANP) ya ce ambaliyar ruwa ta kashe mutum 32 cikin watannin baya-bayan nan.

An ruwaito Yankin Tahoua da ke kudancin ƙasar ne matsalar ta fi ƙamari, inda mutum 12 suka mutu, sai Maraɗi mai mutum 10 da Zandar inda mutane shida suka mutu”, kamar yadda ANP ta ruwaito daga ma’aikatar cikin gida ta ƙasar.

Sai Tileberi mai mutum biyu, da kuma Yamai da Diffa masu mutum ɗai-ɗai.

Rahoton ya ce mutum tara daga ciki sun mutu ne, bayan da gidajen da suke ciki suka rufta akansu, yayin da 23 suka mutu sakamakon nutsewa a cikin ruwan.

Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ake samu cikin tsakiyar kowace damina, na haifar da ɓarna mai yawa a ƙasar.

1 COMMENT

Leave a Reply