Ban sayi motar miliyan ɗari uku ba – Ministan birnin Abuja

Ministan Babban Birnin Tarayya, (FCT Abuja), Nyesom Wike, ya ƙaryata iƙirarin sayan mota ƙirar Lexus LX600 na Naira miliyan 300 da ake zargin an kai masa ofishin.

Mista Wike ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan wata ziyara da ya kai tashar jirgin ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba domin duba aikin gyaran tsarin sufurin jiragen ƙasa na Abuja.

Wasu sassan kafafen yaɗa labarai sun buga hoton wata motaà samfurin SUV mai suna Armored Lexus SUV LX 600, sanye da farantin ‘FCT – 01’.

Rahotanni sun bayyana cewa SUV ɗin da ta kashe sama da Naira miliyan 300 mallakar sabon Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ne.

Amma Mista Wike ya musanta iƙirarin, yana mai bayyana shi a matsayin “ɓarna” kawai, yana mai jaddada cewa an rantsar da shi ranar Litinin kuma bai ma zauna bakin aiki ba tukunna.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a jihar Yobe sun hana sanya wa mota baƙin gilashi da rufe lambar mota

Ya ce duk abin da ya yi shi ne mu’amala da ma’aikata, kuma a yau (Laraba) ya je tashar jirgin ƙasa da ke Abuja tare da ƙaramin ministan babban birnin tarayya Abuja domin ganin al’amura da kansu.

“Yanzu za mu koma ofis don yin mu’amala da kowace ma’aikatun da ke cikin Babban Birnin Tarayya.

“Amma na ga abin da ke faruwa a kafafen sada zumunta na zamani, yadda Babban Sakatare na FCTA ya sayi mota mai tare harsashi ta Naira miliyan 300 da nake amfani da ita.

“Don haka, ina so ku mutane ku je ku buga hannunku a can (a kan motar) ku gani ko motar da aka yi ta nuna wa ce.

“Tare da dukkan girmamawa, ya kamata mutane su yi taka tsantsan don kada su halaka wasu,” in ji shi.

Ya bayyana cewa lokacin da ya koma, babban sakataren dindindin, Adesola Olusade ya shaida masa cewa FCTA na da motocin da ministocin za su yi amfani da su.

“Kuma motar da muke amfani da ita ita ce wannan (ya nuna kan Lexus SUV ta yau da kullum).

“Ban taɓa yarda a siya kowace mota ba, kuma ban yi amfani da wata mota mai tare harsashi ba a hukumance ba.

“Bana amfani da mota mai tare harsashi a matsayina na Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, don haka ya kamata mu bayar da rahoton abin da ya dace, ka da mu halaka kanmu.

“Ina so ku kalli motar da na zo da ita, wadda ke da tuta ku gani ko mota ce mai tare harsashi”, ya tambayi ‘yan jaridun da ke wurin.

A wani labarin kuma, Daraktan yaɗa labarai na ofishin Ministan Anthony Ogunleye, ya yi watsi da iƙirarin da wasu kafafen yaɗa labarai suka yi cewa Wike na shirin ruguza gidaje 6,000 a wasu matsugunai 30 a Abuja, ciki har da Wadata Plaza.

“Muna so mu bayyana cewa waɗannan labaran gaba ɗaya ƙarya ne kuma ba tare da wani tushe ba,” in ji Mista Ogunleye.

Ya bayyana cewa, a ranar 22 ga watan Agusta ne wata jarida ta ƙasa ta ruwaito labarin ruguje gidaje 6,000, tare da taken “Gwamnati na iya ƙwace filaye, ta ruguza gine-gine 6000, da marasa galihu”.

Ya ƙara da cewa wata babbar jarida kuma ta buga abin da ya bayyana a matsayin “labari mai ban haushi”, tare da taken, “Wadata Plaza za ta sauka, ra’ayi ya biyo bayan barazanar rushewar Wike”.

“Don kaucewa shakku, Ministan bai lissafo wurare ko adadin gidajen da za’a cire ba a cikin sanarwar da ya bayar.

“A maimakon haka, abin da ya ba da muhimmanci a koyaushe shi ne cewa za a kawar da matsugunan da ba bisa ƙa’ida ba don amfanin jama’a.

“Equally vexing” shine kanun labarai daga wani gidan yaɗa labarai mai suna cewa, “zan gyara Abuja nan da kwanaki shida” kuma aka danganta hakan ga Ministan Abuja.

“Muna so mu bayyana a fili cewa babu wani lokaci mai girma Ministan ya faɗi haka ko ya yi ishara da wannan magana ta kowace hanya.

Saboda haka, wannan kanun labarai an ɗauke shi ne kawai daga don a ɓata mana suna,” in ji shi.

Sakataren yaɗa labaran ya yi nuni da cewa irin waɗannan rahotanni masu ban sha’awa ba kawai yaudarar jama’a suke yi ba, har ma suna lalata muhimmiyar rawar da aikin jarida sahihi kuma ingantaccen bincike ke takawa a cikin al’umma.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *