Gwamnatin Katsina ta tabbatar da karɓar tallafin biliyan biyu daga Gwamnatin tarayya

A ranar Laraba ne gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da samun Naira biliyan biyu daga cikin naira biliyan 5 da gwamnatin tarayya ta amince wa jihohi.

Bala Salisu-Zango, kwamishinan yaɗa labarai, al’adu da harkokin cikin gida na jihar ne ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani game da jita-jitar cewa gwamnatin tarayya ta saki Naira biliyan biyar ga kowace jiha a faɗin ƙasar.

Ya ce: “An jawo hankalin gwamnatin jihar kan labaran da ke yawo a kafafen yaɗa labarai na cewa gwamnatin tarayya ta saki naira biliyan ga jihohi domin rage raɗaɗi.

“Ina so in bayyana cewa, gwamnatin jihar Katsina ta samu Naira biliyan biyu ne kacal domin sayan hatsi da za a raba wa ‘yan jihar”.

KU KUMA KARANTA: NEMA ta ba da tallafin kayan agaji ga mutane dubu 23 a Nijar

Salisu-Zango ya ce kawo yanzu gwamnatin jihar ta yi amfani da Naira biliyan biyu wajen sayo buhunan shinkafa dubu 40 domin rabawa masu ƙaramin karfi a ɗaukacin rumfunan zaɓe a faɗin jihar.

Ya ce gwamnati za ta kuma yi amfani da kaso na gaba na asusun daga gwamnatin tarayya wajen sayan masara domin rabawa ga magidanta da suka cancanta.

Ya yi gargaɗin cewa gwamnatin jihar za ta ladabtar da duk wanda aka samu yana so a aikin raba kayan agajin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *