Mai gidan haya ta ƙona wadda take zaune a gidanta da ruwan zafi

0
234

Wata mai gidan haya mai suna Amaka Okonkwo ta zuba ruwan zafi gauraye da barkono a kan wata ‘yar haya saboda ƙarin kuɗin haya.

Jaridar Nigerian Tribune ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a Enugwu-Ukwu da ke ƙaramar hukumar Njikoka a jihar Anambara.

A cewar matar mai suna Imabong William, daga jihar Akwa Ibom, wadda a halin yanzu take jinya a asibitin Zion Nawfia, mai gidan, Amaka, ta buƙaci ta bar gidan saboda rashin biyanta sabon ƙarin kuɗin hayar, inda ta ce hayar ta ya ƙare a ƙarshen wata.

Ta bayyana cewa ta buƙaci wani lokaci domin ta samu sabon wuri, amma abin takaici, yayin da take wanke kayanta a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, matar mai gidan ta zuba mata ruwan zafi haɗe da barkono a baya.

KU KUMA KARANTA: Yadda fusatattun matasa suka ƙone mutum biyar da ake zargin ɓarayi ne masu amfani da babur na adaidaita

Duk da cewa an kama wadda ake zargin Amaka Okonkwo, kuma a halin yanzu tana ofishin ‘yan sanda na Nimo, majiyoyi sun ce har yanzu tana alfahari da cewa za ta fita a hannun ‘yan sanda.

Da take mayar da martani ga wannan labari, kwamishiniyar harkokin mata da walwalar jama’a ta jihar, Misis Ify Obinabo, wadda ta garzaya zuwa asibiti inda ake samun jinya, ta gode wa matan Enugwu-Ukwu bisa taimakon da suka yi a kan lokaci.

Kwamishiniyar wadda ta yi magana ta bakin mai taimaka mata, ta yi mata rajistar rashin jin daɗinta kan lamarin tare da yin alƙawarin samun adalci ga wanda abin ya shafa.

Ta yi gargaɗin cewa gwamnatin jihar Anambara ba za ta yi wasa da duk wanda aka samu da laifin cin zarafi ko wane iri ba, ta kuma shawarci jama’a da su riƙa kai rahoton laifuffukan da ba su dace ba ta hanyoyin da suka dace domin shiga cikin gaggawa.

Shugabar ƙungiyar mata ta al’ummar, Lady Chiegbunam Nwosu, ta godewa gwamnatin jihar bisa amsa ƙiran da suka yi, ta kuma bayyana cewa al’ummar ba su goyi bayan wannan mugun nufi da aka yi wa ‘yar haya daga jihar Akwa Ibom.

Mijin wanda ake zargin Mista Ebere Okonkwo, wanda shi ma an gan shi a asibiti bayan an yi masa tambayoyi, ya musanta cewa yana da hannu a cikin lamarin matarsa, inda ya ce duk da cewa yana gida a lokacin da lamarin ya faru, bai san mugun nufin matar sa ba ga ‘yar hayan.

Ƙungiyar ta kuma ziyarci sashin ‘yan sanda na Nimo, inda jami’in ‘yan sandan shiyya ya ba su tabbacin mika lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da bincike mai inganci.

Leave a Reply