Shekaru uku za mu yi akan mulki – Sojin mulkin Nijar

2
305

Daga Ibraheem El-Tafseer

Shugaban mulkin soji a Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya ce gwamnatinsu da ta hamɓarar da shugaba Mohammed Bazoum, ba za ta wuce shekara uku a kan mulki ba.

Janar ɗin ya bayyana haka ne a jawabinsa ga ‘yan Nijar a kafar talabijin ɗin ƙasar, a ranar Asabar da yamma.

Shugaban mulkin sojin kuma ya koka da takunkuman da ƙungiyar Ecowas ta ƙaƙaba wa ƙasar, yana cewa ta yaya za a hana shigar da magunguna cikin ƙasa a bar mutane na mutuwa a asibitoci?

“Ba za a tilasta mu amincewa da abin da ba mu yarda da shi ba,” in ji Tchiani.

KU KUMA KARANTA: Tawagar da ECOWAS ta tura Nijar, ta gana da Bazoum da Tchiani

Ya ƙara da cewa “waɗannan takunkumai sun saɓa wa aƙida da manufar kafa ƙungiyar ta Ecowas ko CEDEAO na ‘yancin kai-komon jama’a da dukiyoyinsu”.

Shugaban sojin ya ce yana tunanin ƙungiyar Ecowas, ba ta auna illar da harin soji zai haddasa a yankin ba.

Tchiani ya ce ƙungiyar ta manta cewa jajircewar sojojin Nijar ce ta hana yankin Afirka ta Yamma aukawa cikin yanayin rashin tabbas.

2 COMMENTS

Leave a Reply