Tawagar da ECOWAS ta tura Nijar, ta gana da Bazoum da Tchiani

3
360

Daga Ibraheem El-Tafseer

Sojojin Nijar na ci gaba da tsare Bazoum a fadar gwamnatin ƙasar tun bayan kifar da gwamnatinsa ranar 26 ga watan Yuni.

Tawagar ECOWAS ta musamman da ta ziyarci Nijar ta samu ganawa da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum da shugabannin mulkin sojin ƙasar a wani yunƙuri na maido da hamɓararren shugaban ƙasar kan karagar mulkin ƙasar.

Tawagar masu shiga tsakanin, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya janar Abdulsalamu Abubakar mai ritaya, da mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya Muhammad Sa’ad Abubakar lll, ta samu ganawa da shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Abdourahamane Tchiani.

Ziyarar masu shiga tsakanin na zuwa ne kwana guda bayan da manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Ecowas suka ce sun saka ranar auka wa Nijar da yaƙi, matsawar sojojin ba su mayar da Bazoum kan mulki ba.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Nijar sun amince su tattauna da ECOWAS

Sojojin mulkin sun tattauna da tawagar ECOWAS ɗin a birnin Yamai, to sai dai ba su yi bayani abubuwan da suka tattauna ba.

Tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ɗaukar dubban ‘yan sa kai domin kare ƙasar daga farmakin ECOWAS.

ECOWAS na son sojojin su mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan mulki, wanda suke tsare da shi tun 25 ga watan Yuli.

Juyin mulkin da dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa suka yi wa Bazoum ranar 26 ga watan Yuli, ya janyo zazzafan mataki daga ECOWAS.

Komawar kwamitin na zuwa ne kwana ɗaya bayan ECOWAS ta ce taron manyan hafsoshinta na kwana biyu a birnin Accra ya saka ranar kai yaƙi Nijar.

Kwamishinan harkokin siyasa na ECOWAS, Ambasada Abdel-Fatau Musah ya ambato su, suna cewa: “Mun shirya shiga a duk lokacin da aka ba mu umarni”.

Amma dai, Ecowas ta jaddada cewa duk da wancan mataki ƙofofin sulhunta rikici ta hanyar diflomasiyya za su ci gaba da kasancewa a buɗe.

A baya, wa’adin ECOWAS da ƙoƙarin diflomasiyya ba su iya tanƙwara sojoji masu mulki a Nijar ba wajen mayar da hamɓararren Shugaba Bazoum kan karagar mulki.

Wata majiya a cikin kwamitin diflomasiyyar na ECOWAS, ƙarƙashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), ta ce saɓanin ziyarar farko, a wannan karo suna sa ran samun kyakkyawar tarba daga shugabannin mulkin sojan Nijar.

A karon farko, rahotanni sun ce kwamitin Abdulsalami Abubakar bai samu kyakkyawar tarba a Yamai ba, hasali ma jami’an diflomasiyyar ba su iya shiga gari ba, daga filin jirgin saman Diori Hamani.

Babu masaniya a kan irin tuntuɓa ta bayan fage da aka ci gaba da yi kan rikicin siyasar na Nijar kafin wannan lokaci, amma majiya daga kwamitin ta ce suna da ƙwarin gwiwa a wannan karo za su gana da Janar Abdourahamane Tchiani.

Ta ce: “Duk da yake ECOWAS ta cimma waccan matsaya a birnin Accra, amma har yanzu babu wanda yake son yin yaƙi.”

3 COMMENTS

Leave a Reply