Hukumar NSCDC a Legas, ta kama masu safarar mutane a wani otel

1
189

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas da ke kula da jami’an tsaro da tsaron farin kaya, NSCDC, a ranar Litinin ta ce ta kuɓutar da wasu ‘yan mata huɗu masu ƙarancin shekaru daga wani Motel da ke ƙauyen Totomu, kusa da iyakar Legas da Ogun.

Kwamandan rundunar, Usman Alfadarai, ya ce an kai farmakin ne da misalin ƙarfe 11:53 na safiyar ranar 11 ga watan Agusta.

A cewarsa, sashin yaƙi da fataucin bil adama sun yi aiki da sahihan bayanan sirri tare da ci gaba da sa ido don kai farmaki kan otal ɗin.

Ya ce, an gano a otal ɗin anayin lalata da ‘yan mata masu ƙarancin shekaru domin yin karuwanci da kuma yin aiki domin a biya su.

KU KUMA KARANTA: Hukumar EFCC ta kama maɓoyar ‘Yahoo-Yahoo’ a Benuwe, ta kama mutane 14 da ake zargi

“Huɗu da abin ya shafa, wanda ‘yan shekaru tsakanin 15 zuwa 17, an yi nasarar ceto su daga harabar,” in ji shi, ya ƙara da cewa an kama wata mace da ake zargi.

A cewar kwamandan rundunar, wanda ake zargin da waɗanda aka ceto za a miƙa su ga hukumar hana fataucin mutane ta ƙasa, NAPTIP, domin ci gaba da bincike.

Mista Alfaradai ya ce, a wannan rana, tawagar ‘yan sintiri ta Corps’ da aka tura domin sa ido kan kamfanin man fetur na Najeriya, bututun mai na NNPC sun yi nasarar daƙile wani yunƙurin ɓarna a Idimu, Legas.

Ya ce an kama wanda ake zargin kuma za a gurfanar da shi gaban kotu bayan kammala bincike.

1 COMMENT

Leave a Reply