Boko Haram a Borno sun yi garkuwa da mata bakwai, sun kashe biyar

2
295

Wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun kai farmaki kan ayarin motocin da ke ɗauke da kayayyaki da fasinjoji a ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno, inda suka kashe mutane biyar tare da sace mata bakwai.

An kai harin ne ranar Alhamis kan ayarin motocin jami’an tsaro da ke ɗauke da manyan motoci da ke kusa da garin Banki da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru a ƙaramar hukumar da misalin ƙarfe 2:30 na rana.

Wata majiya mai tushe da ke tafiya a kan hanyar Maiduguri zuwa Bama zuwa Banki mai suna Babagana Kaumi, ta tabbatar wa da jaridar ta PUNCH ta wani saƙo mai sauti kamar haka: “ ayarin motocin fasinjoji da kaya sun yi kwanton ɓauna a kusa da Banki.”

KU KUMA KARANTA: Boko Haram sun kashe manoma 15 a jihar Borno

Ya ci gaba da cewa: “Ɗaya daga cikin motocin ta samu matsala, kuma idan irin haka ta faru duk sojoji sun maida hankalinsu kan motar da ta lalace har sai an gyara ta kafin a ci gaba da tafiya.

“Abin da ya faru ke nan a ranar; yayin da sojojin suka mayar da hankalinsu kan wata motar da ta samu matsala, maharan sun kai hari inda suka kashe matafiya biyu, direban ɗaya daga cikin motocin da mataimakansa biyu sun yi awon gaba da mata kusan bakwai tare da ƙona ayarin motocin.”

Kaumi ya ce “A kwanakin baya, maharan sun far wa irin waɗannan ayarin motocin ne kawai, suna ƙwace kuɗi da duk wani abu mai daraja, ciki har da kowane irin takalmi mai kyau daga masu ababen hawa, inda suka ci gaba da tafiya a raye ba tare da wani rauni ba; amma a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, sun kai farmaki cikin fushi.”

Ya ce hare-haren Boko Haram a yanzu sun ƙara ƙamari a sassan Najeriya da Kamaru na kan iyaka.

Har yanzu hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba.

2 COMMENTS

Leave a Reply