Ya fashe da kuka bayan ya sayar da akuyarsa

0
291

Ya fashe da kuka bayan ya sayar da akuyarsa

Daga Haruna Abdulrashid Gombe

Wani abin tausayi da mamaki da ya faru a tiken dake kusa da Jami’ar jihar Gombe (GSU)

Wani Bawan Allah ya je kasuwar da Akuya domin ya sayar. Ya sayar aka bashi kuɗin, sai kuma ya fashe da kuka a wajen. Mutumin da ya sayi akuyar yace da shi: “Bawan Allah kukan meye kuma za kayi kai da ka samu kuɗi an sayi abunka?”

Mutumin cikin kuka sai yace, “Wallahi sato Akuyar na yi ba tawa bace, shiyasa nake kuka. Dalilin satarta kuwa, yau kwana uku ba’a ɗora tukunyar abinci a gidana ba”

Mutumin da ya sayi Akuyar da ya ji haka, kuma da yake shima bawan Allah ne, sai ya bar mishi kuɗin, yace da shi ya nemo mai Keke NAPEP, ya kwatanta mishi inda ya ɗauko Akuyar su mayar wa mai shi.

KU KUMA KARANTA: Francisco Domingo Joaquim ya fi kowa girman baki a duniya

Aka kuwa ƙira mai NAPEP aka ɗauki Akuyar zuwa inda wanda ya kawo ta ya bayyana musu. Suna zuwa wata kwanar da ya nuna musu, sai su saketa ta koma gidan su.

Wannan alama ce a yau ana cikin yanayi da mutane ke buƙatar tallafi. Shugabannin mu susan yana da kyau ayi wani abu akan matsalar da Talakawa ke ciki a ƙasarnan domin abun ya kai yadda ya kai wallahi.

Leave a Reply