Connect with us

Ƙasashen Waje

Amurka za ta ɗora alhakin kare lafiyar Bazoum a hannun sojojin Nijar

Published

on

Amurka za ta ɗorawa gwamnatin mulkin sojan da ta karɓi mulki a Jamhuriyar Nijar alhakin kare lafiyar zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum, da iyalansa, da kuma tsare wasu jami’an gwamnati.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a wata sanarwa da ya fitar ya ce “Amurka ta bi sahun ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) wajen yin ƙira da a maido da tsarin mulki a Nijar.”

A baya-bayan nan ne Amurka ta dakatar da wasu shirye-shiryen ba da taimako ga ƙasar Nijar bayan da sojoji suka hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ta dimokraɗiyya.

KU KUMA KARANTA: Idan sojojin ECOWAS suka yaƙe mu, za mu kashe Bazoum – Jagororin juyin mulkin Nijar

A ranar alhamis ne ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta ba da umarnin ƙaddamar da wata rundunar da za ta yi amfani da su wajen yaƙar gwamnatin mulkin sojan da ta karɓi mulki a Nijar a watan Yuli.

Ta ce tana son a maido da mulkin dimokuraɗiyya cikin lumana amma dukkan zaɓukan ciki har da ƙarfi na kan teburin.

A cewar Blinken, Amurka ta yaba da yunƙurin da ECOWAS ta yi na gano duk wani zaɓi na warware rikicin cikin lumana.

Barazanar mamayewa, ko da yake ba a fayyace ta ba, ya ta da tarzoma a ciki da wajen Nijar, mai samar da sinadarin Uranium, wanda har zuwa lokacin juyin mulkin, ya kasance muhimmiyar aminiyar ƙasashen yammacin duniya wajen yaƙi da masu kaifin kishin Islama dake lalata yankin Sahel.

Gwamnatin mulkin sojan da ta karɓe mulki a ranar 26 ga watan Yuli, ta ƙi amincewa da wa’adin da ƙungiyar ta ECOWAS ta ƙayyade a ranar 6 ga watan Agusta, maimakon haka ta rufe sararin samaniyar Nijar tare da sha alwashin kare ƙasar daga duk wani hari da aka kai daga ƙasashen waje.

Ƙungiyar ta yi alƙawarin aiwatar da takunkumi, hana tafiye-tafiye da kuma daskare dukiyoyi a kan waɗanda ke hana komawa kan karagar mulkin Bazoum.

2 Comments

2 Comments

  1. Pingback: Ƙasar Rasha ta gargaɗi ƙungiyar ECOWAS game da ɗaukar matakin soji | Neptune Prime Hausa

  2. Pingback: Za mu kai Bazoum kotu saboda cin amanar ƙasa – Sojojin Nijar | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Bankin duniya ta baiwa Togo kyautar dala miliyan 200 don magance matsalar lantarki

Published

on

Bankin duniya ta baiwa Togo kyautar dala miliyan 200 don magance matsalar lantarki

Bankin duniya ta baiwa Togo kyautar dala miliyan 200 don magance matsalar lantarki

Bankin Duniya ta amince da bai wa Togo dala miliyan 200 don magance matsalar samar da wutar lantarkin da kasar ke fama da ita na tsawon watanni.

A dai-dai lokacin da za a fara babban zaɓen ƙasar, a ƴan watannin nan, Togo na fuskantar matsananciyar matsalar rashin wutar lantarki, lamarin da ya haddasa tsadar rayuwa a ƙasar.

Ministan tattalin arziki da kuɗin Togo, Sani Yaya, ya bayyana farin cikinsu game da samun wannan tallafi, sannan ya ce kudin zai agaza wurin gina manyan layin wuta wanda hakan zai taimaka wa ƴan ƙasar da ke rayuwa a ƙauyuka wajen samun wutar cikin sauƙi.

Ministan ya ƙara da cewa wannan tallafi zai sa sama da mutane miliyan ɗaya da rabi su samu wutar lantarki mara katsewa.

KU KUMA KARANTA: Bankin Duniya na gargaɗi kan ‘matsananciyar yunwa’ a Gaza

Matsalar ƙarancin wutar da aka fuskanta na zuwa ne bayan Najeriya wacce ita ce ke bai wa Togon da Nijar da kuma Benin lantarki ta bayyana takaita adadin wutar da za ta dinga ba su a ranar 1 ga watan Mayun shekarar nan.

Hukumar da ke kula da wutar lantarkin ta ce Najeriya wacce ita ce ta fi ba su wutar na bin su bashin miliyoyin daloli na lantarkin da suka sha kuma suka kasa biya.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Mutane da dama sun mutu a wani harin bam a Somalia

Published

on

Mutane da dama sun mutu a wani harin bam a Somalia

Mutane da dama sun mutu a wani harin bam a Somalia

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon tashin bam a wani gidan cin abinci da ke Mogadishu babban birnin ƙasar Somaliya ya haura zuwa mutum tara, kamar yadda majiyoyin tsaro suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Litinin.

Lamarin ya faru ne bayan da wata mota maƙare da bam ta tarwatse a gidan abincin inda masoya ƙwallon ƙafa da suka je kallon wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2024.

”Fararen-hula 9 ne suka mutu, yayin da mutum 20 kuma suka jikkata sakamakon tashin bam ɗin,” a cewar wani jami’in hukumar tsaron ƙasar Mohamed Yusuf, adadin da ya ƙaru daga mutum biyar da hukumomi suka sanar ranar Lahadi da daddare.

“Akwai mutane da dama a wurin cin abincin, yawancinsu matasa ne da ke kallon wasan ƙwallon kafa. Muna godiya ga Allah kan cewa mafi yawansu sun samu hanyar fita da ransu cikin lafiya bayan da suka yi amfani da tsani wajen haurawa ta bayan katangar ginin wurin,” in ji shi.

KU KUMA KARANTA: Faɗa da ruwan bama-bamai a birnin Gaza bayan ba da umarnin kwashe jama’a

Hotunan da aka wallafa a shafukan intanet sun nuna yadda wuta da hayaƙi suka turnuke sama bayan da bam ɗin ya tashi a cikin shahararren wurin cin abinci da ke tsakiyar birnin.

Wani ɗan sanda Mohamed Salad da ya gane wa idonsa lamarin da ya faru ‘yan mintoci kaɗan bayan tashin bam ɗin ya shaida wa kamfanin dillacin labaran AFP cewa an gano gawawwaki da dama a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin.

”Mutane biyar ne suka mutu a wajen ginin da kuma kan babban titi ciki har da direbobin motocin da ke wucewa ta hanyar wurin da lamarin ya auku,” in ji shi.

Munanan ayyukan ta’addanci
“Mutane huɗu ne suka mutu a cikin gidan abincin, an ciro wasu daga cikin ɓaraguzan gini,” in ji jami’in.

Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma kamfanin dillancin labarai na ƙasar Somaliya ya ce mayaƙan ƙungiyar ta’addanci ta Al-Shabaab ne suka kai harin.

Ƙungiyar Al-shabaab dai ta shafe fiye da shekaru 17 tana kai hare-haren ta’addanci kan gwamnatin Somaliya a Mogadishi da wasu sassan ƙasar.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Jami’ai a Gaza sun zaƙulo gawawwakin Falasɗinawa 21 daga cikin ɓaraguzai

Published

on

Jami'ai a Gaza sun zaƙulo gawawwakin Falasɗinawa 21 daga cikin ɓaraguzai

Jami’ai a Gaza sun zaƙulo gawawwakin Falasɗinawa 21 daga cikin ɓaraguzai

Jami’an kare farar hula a Gaza sun zaƙulo gawawwaki 21 na Falasɗinawa daga cikin ɓaraguzai a ranar Lahadi bayan wani hari da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza.

Wata majiya daga ɓangaren kiwon lafiya ta bayyana cewa an gano gawar mutum shida sakamakon harin da Isra’ila ta kai a birnin Rafah inda aka kai su asibitin Khan Younis.

Haka kuma an ƙara zaƙulo wasu gawawwakin uku daga cikin ɓaraguzai a yammacin Gaza, kamar yadda Hukumar Kare Fararen Hula ta Gaza ta bayyana a wata sanarwa.

READ ALSO: Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 29 a harin da ta kai a wata makaranta a Gaza

Jami’an sun ƙara gano wasu gawawwakin goma a unguwar Tel al-Hawa da ke kudu maso yammacin Gaza.

Sai kuma mazauna sansanin gudun hijira na Nuseirat sun gano gawawwakin mutum biyu a tsakiyar Zirin Gaza, kamar yadda shaidu suka bayyana.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like