Idan sojojin ECOWAS suka yaƙe mu, za mu kashe Bazoum – Jagororin juyin mulkin Nijar

Daga Ibraheem El-Tafseer

Tabbas, idan Sojojin ECOWAS suka saka mana ƙarfi, suka yaƙe mu, to babu makawa za mu hallaka Bazoum
Jagororin da suka jagoranci kifar da gwamnatin dimukuraɗiyya a Jamhuriyyar Nijar, sun yi barazanar hallaka shugaba Mohammed Bazoum muddin ƙasashen da ke maƙwafta da su ko kuma ECOWAS ta auka musu da ƙarfin soja.

Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa ECOWAS a ranar Alhamis ta umarci dakarunta na ko-ta-kwana da su kimtsa su ja ɗamarar fara yaƙi domin dawo da mulkin dimukuraɗiyya a jamhuriyyar Nijar.

Rahoton AP ya labarto cewa wani jami’in sojan ƙasashen yamma, ya shaida bisa sharaɗin ba za’a bayyana sunansa ba cewa, wakilan dakarun Junta sun tabbatar wa mataimakin sakataren wajen Amurka Victoria Nulanda irin barazanar da shugaba Bayou ke fuskanta a lokacin da ta ziyarci ƙasar a ciki makon nan.

Sannan, wani jami’in Amurka shi ma ya tabbatar da wannan, yayin da ke magana bisa neman a sakaye sunansa saboda ba shi ne ke da ikon magana da ‘yan jarida ba.

KU KUMA KARANTA: Khalifa Muhammad Sanusi II ya kai ziyara Nijar, don sasantawa (bidiyo)

Barazanar daga dukkanin ɓangarorin ya haifar da zaman ɗar-ɗar, sai dai an yi fatan dukkaninsu ba za su kai ga aiwatar da kalaman nasu ba, kamar yadda tsohon jami’in ofishin jakadancin Amurka, Aneliese Bernard ya shaida, wanda shi ɗin masani ne kan harkokin Afirka.

LEADERSHIP ta labarto cewa ECOWAS ta gudanar da wani taro a ranar Alhamis a Abuja dangane da matakinta na gaba da za ta ɗauka kan halin da ake ciki a Nijar.

Da yake magana bayan kammala ganawar tasu, shugaban hukumar ECOWAS, Omar Alieu Touray, ya ce, sun bi matakan lalama da salama amma haƙarsu ba ta cimma ruwa ba wajen maido da shugaba Bazoum kan mulkinsa, don haka ne suka cimma matsayar umartar sojojinsu na ko-ta-kwana da su shirya ɗamarar yaƙi.

Ya kuma ɗaura laifin dukkanin wani ƙunci da takunkumin da aka ƙaƙaba wa Nijar ya janyo wa jama’ar ƙasar, ya kuma ce, matsayar da suka cimma zai zama haɗin guiwa ne.


Comments

One response to “Idan sojojin ECOWAS suka yaƙe mu, za mu kashe Bazoum – Jagororin juyin mulkin Nijar”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Idan sojojin ECOWAS suka yaƙe mu, za mu kashe Bazoum – Jagororin juyin mulkin Nijar […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *