Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda, gungun ‘yan Boko Haram sun miƙa wuya

2
384

Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Haɗin Kai a arewa maso gabas, (OPHK), sun yi nasarar kai wani harin kwantan ɓauna a mashigar ‘yan ta’addan Boko Haram da ke kan hanyar Kuka a ƙaramar hukumar Konduga a jihar Borno.

Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Birgediya janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis a Abuja.

Mista Nwachukwu ya ce sojojin sun yi wa ‘yan ta’addan kwanton ɓauna, kafin daga bisani su yi musayar wuta da su inda suka kashe biyu yayin da wasu suka tsere cikin ruɗani.

Ya ce sojojin sun ƙwato harsashi 63 na alburusai 12.7, na’urar fashewa guda ɗaya, harsashi na IED, alluran Pento guda biyar da kuma kuɗi N19,460.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun kashe ‘yan fashi 10 tare da ceto mutane tara a Zamfara

“Hakazalika, bayan farmakin da sojoji suka kai wa yankunan ‘yan ta’addan Boko Haram, wani ɗan ta’adda ya miƙa wuya ga sojojin bataliya ta 222 a Geizuwa a ƙaramar hukumar Konduga.

“Kayan da aka ƙwato daga hannun wanda ake zargin sun haɗa da bindiga ƙirar AK47 ɗaya, mujalla ɗaya da harsashi na musamman 7.62mm har guda 26.

“A halin yanzu wanda ake zargin yana ci gaba da bincike don ci gaba da ɗaukar matakin da ya dace. “Shugaban hafsan soji, Lutanar Janar Taoreed Lagbaja, ya ya ba da matakin da sojojin ke da shi na taka-tsantsan da ruhin faɗa.

“Ya buƙace su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu tare da tabbatar da cewa an kawar da ragowar ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a yankunan da suke da alhakin,” in ji Mista Nwachukwu.

2 COMMENTS

Leave a Reply