Khalifa Muhammad Sanusi II ya kai ziyara Nijar, don sasantawa (bidiyo)

1
253

Daga Haruna Abdulrashid

Tun bayan juyin mulki da sojoji suka yi a ƙasar Jamhuriyar Nijar ba’a yi wani baƙon da kowane ɓangaren al’umman wannan ƙasar suka yi maraba da zuwan shi ba irin Sarkin Kano na 14 Khalifa Sunusi Lamiɗo Sunusi ba.

Khalifa Sanusi ya samu tarba daga Sarkin Damagaram Muhammadu, wanda ya yi murna bayan rashin ganinsa na wani lokaci.

Haka ma ya ga farin cikin tarya daga ɓangaren gwamnatin Sojoji dake riƙe da mulkin ƙasar har da ɓangaren magoya bayan Shugaba Bazoom da al’umman ƙasar baki ɗaya, yayin da dubun dubatan al’umman ƙasar Nijar suka tarbe Sarki Sunusi Lamiɗo Sunusi.

Al’umma na fatan wannan ziyarar tashi ta zamo sanadin samun daidaito akan wannan lamarin.

Kalli bidiyo a nan:

1 COMMENT

Leave a Reply