Za’a ƙara farashin man fetur, saboda tashin dala

Daga Ibraheem El-Tafseer

Za a iya cewa har yanzu tsugune ba ta ƙare wa ‘yan Najeriya ba, game da matsalar tattalin arziƙi da suke fuskanta.

Wannan kuwa ya biyo bayan tashin farashin da ake fuskanta na dalar Amurka wanda ke ƙara ta’azzara abubuwa a Najeriya.

Kusan farashin komai a ƙasar ya ta’allaƙa ne da farashin dala, saboda kusan komai shigar mata da shi take daga ƙasashen ƙetare.

Hakan ya haifar da jita-jita cewa farashin man fetur da ake sayarwa a naira 617 a yanzu zai ƙara tashi.

Dalilin da ya sanya ƙungiyar manyan dillalan man fetur na ƙasa wato IPMAN ta mayar da martani kan wannan jita-jita.

KU KUMA KARANTA: Masu sayar da man fetur na arewa sun yi barazanar shiga yajin aiki

Chinedu Okoronkwo shi ne shugaban ƙungiyar na ƙasa ya ce “matuƙar dala za ta tashi farashin man fetur zai tashi shi ma”.

“Ba ma iya samun dala a bankunan kasuwanci kuma idan kaje kasuwar bayan fage farashin ya wuce duk yadda kake zato,” in ji Chinedu.

Shugaban ƙungiyar reshen jihar Kano, Bashir Ɗan Mallam, ya shaida wa BBC cewa “a yanzu farashin mai ya tashi a Legas da wurare da yawa, yanzu fa masu gidajen mai sai dai su haɗa hannu su sayi mota guda”.

“Ta yaya za mu iya tunkarar mutanen Najeriya da wannan tsada, ina ganin sai dai mu rufe gidanjen man, mu zuba wa sarautar Allah ido,” in Bashir Ɗanmalan.

Man da ake saya daga waje zuwa Najeriya ana sayansa ne da dalar Amurka, wadda farashinta ya haura naira 940 a cewar wani ɗan kasuwa da ke Legas a Najeriyar.

Tashinta kuma zai iya haifar da tashin farashin mai wanda shi kuma ake sayar da shi a naira 617, kuma ba a san ko nawa zai iya komawa ba idan ƙarin da ake tsammani ya auku.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed TInubu ne dai ya sanar da cire farashin mai a ƙasar, a ranar da aka rantsar da shi a matsayin shugaba.

Kuma tun bayan nan farashin abubuwa ke ƙara ta’azzara a ƙasar.


Comments

One response to “Za’a ƙara farashin man fetur, saboda tashin dala”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Za’a ƙara farashin man fetur, saboda tashin dala […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *