Wasu da ake nema ruwa a jallo, sun miƙa wuya ga ‘yan sanda a Kano

0
247

Nasiru Abdullahi, wanda aka fi sani da Chile Maidoki, wanda yana ɗaya daga cikin manyan mutane uku da ke cikin jerin sunayen ‘yan sandan jihar Kano da ake nema ruwa a jallo, ya miƙa kansa ga kwamishinan ‘yan sanda, Mohammed Usaini Gumel.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya bayar da rahoton cewa, Chile Maidoki, ɗan Layin Falwaya Kurna, na daga cikin manyan mutane uku da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Gumel ya bayyana da ladar N100,000 kowanne.

Sai dai ya kai kan sa a hedikwatar ‘yan sandan jihar Kano ta Bompai a ranar Asabar.

Miƙa wuyan Chile Maidoki ya kawo adadin tubabbun masu laifi 100 da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammad Gumel ya karɓa, a cewar wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa, ya kuma bayyanawa manema labarai a ranar Asabar.

KU KUMA KARANTA: An kama ‘yan sanda, FRSC, LASTMA da ‘yan daba 14 bisa laifin karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba

“Chile Maidoki ya shaida wa ‘yan sanda cewa ya kan kwana a maƙabartar da ke cikin birnin Kano don kawai kar jami’an tsaro su gano shi.

“Yanzu yana ƙira ga ‘yan sanda da mutanen jihar da su gafarta masa, cewa ya tuba kuma a yanzu a shirye yake ya yi aiki da ‘yan sanda don inganta zaman lafiya da ci gaba a jihar,” Mista Kiyawa ya bayyana.

Don haka bai kamata jama’a su guje shi ba.

“Duk da haka, sauran biyun, tare da ladan naira dubu 100 ga kowannen su, da duk wanda ya samu bayanai da suka kai ga kama su, don har yanzu ana neman su,” inji shi.

Su ne Abba Burakita na Ɗorayi Quarters da Hantar Daba na Kwanar Disu.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Waɗanda za su ci gajiyar waɗannan kyaututtukan tare da sahihan bayanai kan inda suke ana buƙatar su tuntuɓi ofishin ‘yan sanda mafi kusa.”

Leave a Reply