An kama ‘yan sanda, FRSC, LASTMA da ‘yan daba 14 bisa laifin karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba

2
200

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta cafke wasu jami’anta uku da ke karɓar kuɗin fansa, da takwarorinsu na hukumar kiyaye haɗurra ta tarayya da kuma hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas da ke aiki da ‘yan daba.

An kama su ne a unguwar Mile 2 tsakanin Juma’a da Asabar tare da wasu ‘yan daba 14, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin ya bayyana a ranar Asabar a Ikeja.

Mista Hundeyin ya bayyana cewa an kama mutanen ne a wani samame da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Fatai Tijani ya jagoranta.

Ya ƙara da cewa kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas, Idowu Owohunwa, ya kafa wata runduna ta musamman, wacce ta gudanar da aikin, biyo bayan rahotannin da wasu ‘yan daba da wasu jami’an tsaro na bin doka da oda suke yi wa masu ababen hawa kwata-kwata ba ƙaƙƙautawa.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun daƙile harin ‘yan bindiga a ofishin ‘yan sanda da masallaci a Zamfara

“Da yake da niyyar duba yadda ake samun ƙaruwar satar dukiyar jama’a a kan manyan tituna, CP Idowu Owohunwa, ya kafa wata tawaga ta jami’an tsaro, tare da ba da umarnin kai samame wuraren da aka gano cewa sun yi ƙaurin suna wajen aikata munanan ayyuka.

“Tawagar ‘yan sandan da ta fara kai samame a ranar Juma’a, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ne ya jagoranta, kuma ta ƙunshi ƙungiyoyin dabaru da jami’an ‘yan sanda daga hedikwatar jihar.

“Rundunar ta kasance a yankin Mile 2 na jihar, wurin da ake karɓar kuɗin fansa,” in ji Hundeyin.

Ya ƙara da cewa Owohunwa yana gargaɗin cewa duk wani jami’in tsaro, ba tare da la’akari da hukumar ba, da aka samu da hannu wajen satar dukiyar jama’a, za a kama shi kuma a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.

Mista Hundeyin ya ƙara da cewa “CP ya yi wa masu ababen hawa alƙawarin cewa rundunar za ta ci gaba da kula a wasu sassan jihar har sai an sun ga sun daina.”

2 COMMENTS

Leave a Reply