Za mu sake duba biyan albashin ma’aikatan gwamnati – Tinubu ga shugaban bankin duniya

1
143

Daga Nusaiba Hussaini

Shugaba Bola Tinubu ya ce ana ci gaba da binciken ƙwaƙwaf na babban bankin Najeriya (CBN).

Shugaban ya kuma ce ana shirin yin garambawul a kan albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Tinubu ya yi magana ne a ranar Juma’a a fadar shugaban ƙasa yayin ganawa da Ajay Banga, shugaban bankin duniya.

“Ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi a babban bankin. Za mu yi nazari sosai kan tsarin albashin ma’aikatan gwamnati,” in ji Tinubu a wata sanarwa ɗauke da sa hannun Ajuri Ngelale, mashawarcinsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai.

“Ba zan iya yarda da alƙaluman da nake gani ba kuma na taɓa samun irin wannan ƙwarewa a matakin jiha.“Gwamnatin ta zo daidai da sauƙin tsarin kasuwanci a Najeriya. Za mu toshe duk mabuɗin kuɗi, gyare-gyaren za a yi niyya ne a kan yadda muke aiki, canza halaye da kuma daidai da ilmantar da jama’armu. Yana da tsada amma za mu yi. “

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya ta shirya gyaran hanyar jirgin ƙasa na Abuja, zai lanƙwame naira biliyan biyar

A kwanakin baya jaridar TheCable ta ruwaito cewa shugaban ƙasar ya naɗa Jim Obazee, tsohon babban jami’in gudanarwa na hukumar bayar da rahoton kuɗi na Najeriya, domin ya binciki CBN da sauran su.

Tinubu ya kuma ce ya kamata cibiyar Bretton Woods ta kalli ƙasar nan a matsayin mai taka rawa a fagen duniya, ba wai kawai a matsayin ƙasa mai fama da matsalar tattalin arziƙi ba.

“Muna tsaye a matsayin al’umma mai fa’ida kuma mai ilimi, muna neman kawar da hargitsi ta hanyar dabaru. Haɗin gwiwar ku ya yi daidai da neman haɗin gwiwa, kuma tare, za mu ci gaba da amfanar juna wanda zai wadatar da mu duka,” in ji shi.

Shugaban ya yi ƙira da a ƙara tallafi daga bankin duniya domin rage raɗaɗin talauci a ƙasar.

Tinubu ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali ne kan sauye-sauye masu yawa, kamar ƙarfafa gyare-gyare a harkar man fetur, da samar da sauƙin gudanar da kasuwanci, da ba da fifiko kan harkokin tsaro domin bunƙasa kuɗaɗen shiga.

A nasa ɓangaren, Banga ya yabawa Tinubu kan ƙoƙarin da yake yi na magance ƙalubalen tattalin arziƙin ƙasar.

1 COMMENT

Leave a Reply