Daga Nusaiba Hussaini
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana dalilin da ya sa ya janye sunan Dakta Maryam Shetty daga Kano a matsayin minista, tare da maye gurbinta da sabon zaɓaɓɓen Dakta Mairiga Mahmud, ita ma daga Kano.
Tinubu ya kuma gabatar da Mista Festus Keyamo don ganin Majalisar Dattawa ta amince da shi a matsayin Ministan Tarayyar Najeriya.
A cikin wata wasiƙa da ya aike wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kuma aka karanta a zauren taron na ranar Juma’a, shugaba Tinubu ya ce:
“Ina bin tanadin sashe na 147 ƙaramin sashe na 2 na ƙundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 kamar yadda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka na yanke shawarar janye sunan Dakta Maryam Shetty a matsayin wanda aka zaɓa.
KU KUMA KARANTA: Tinubu ya sake aike wa da sabbin sunayen ministocin, ciki har da tsoffin gwamnoni 5
“Bugu da ƙari, ina jin daɗin naɗa Dakta Mariga Mahmud da Mista Festus Keyamo don tantancewa Majalisar Dattawa kuma, idan ta dace, a tabbatar da su a matsayin ministoci.
“Ina fata da gaske cewa Majalisar Dattawa za ta yi la’akari kuma ta amince da buƙatar da ke sama. Mai girma Shugaban Majalisar Dattawa da kuma Sanatoci masu girma, don Allah ku yarda da irin tabbacin da nake yi min.” Inji Tinubu.
[…] KU KUMA KARANTA: Dalilin da ya sa na janye sunan Maryam Shetty a matsayin minista – Tinubu […]