‘Yan sanda a Malawi sun ceto wata jaririya da mahaifiyarta mai shekaru 21 mai suna Olivia Jonas ta binne da ranta a unguwar Lunzu da ke Blantyre.
A cewar kafar yaɗa labaran Malawi24, jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan, Sajan Jonathan Phillipo, ya yi iƙirarin cewa wadda ake zargin tana ɗauke da juna biyu na wata takwas a lokacin da ta haifi ɗiya mace a gida sannan ta binne jaririyar a wani daji da ke kusa ba tare da sanar da kowa ba.
KU KUMA KARANTA: Bayan kwana uku da binne shi, an tono shi, an same shi da ransa
Rahotanni sun bayyana cewa, lokacin da mijinta ya dawo gida daga aiki, ta shaida masa cewa cikin ta ya zube, kuma an kai ta asibiti domin yi mata magani.
A cewar ‘yan sandan, Jonas ta yi iƙirarin cewa ta haifi jaririyar a mace kuma ta binne ta a wani daji da ke kusa da wurin bayan da ma’aikatan jinya da ke kula da ita suka yi mata tambayoyi.
Wanda ake zargin ta jagoranci jami’an ‘yan sanda da jami’an lafiya tun daga asibitin zuwa inda ta binne jaririyar, inda aka tono wurin kuma aka gano cewa jaririyar tana nan da rai kuma cikin koshin lafiya.
A halin yanzu, wacce ake zargin, wacce ake sa ran za ta amsa tambayoyi akan ɓoye haihuwar yarinya, tana kwance a asibiti inda take jinya.Wata mata ta binne jaririn da ta haifa da rai a cikin daji
‘Yan sanda a Malawi sun ceto wata jaririya da mahaifiyarta mai shekaru 21 mai suna Olivia Jonas ta binne da ranta a unguwar Lunzu da ke Blantyre.
A cewar kafar yaɗa labaran Malawi24, jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan, Sajan Jonathan Phillipo, ya yi ikirarin cewa wadda ake zargin tana ɗauke da juna biyu na wata takwas a lokacin da ta haifi ɗiya mace a gida sannan ta binne jaririyar a wani daji da ke kusa ba tare da sanar da kowa ba.
Rahotanni sun bayyana cewa, lokacin da mijinta ya dawo gida daga aiki, ta shaida masa cewa cikin ta ya zube, kuma an kai ta asibiti domin yi mata magani.
A cewar ‘yan sandan, Jonas ta yi ikirarin cewa ya haifi jaririyar a mace kuma ta binne ta a wani daji da ke kusa da wurin bayan da ma’aikatan jinya da ke kula da ita suka yi mata tambayoyi.
Wanda ake zargin ta jagoranci jami’an ‘yan sanda da jami’an lafiya tun daga asibitin zuwa inda ta binne jaririyar, inda aka tono wurin kuma aka gano cewa jaririyar tana nan da rai kuma cikin koshin lafiya.
A halin yanzu, wacce ake zargin, wacce ake sa ran za ta amsa tambayoyi akan ɓoye haihuwar yarinya, tana kwance a asibiti inda take jinya.