No menu items!

Sample Page Title

Date:

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Nasser Kanaani a ranar Litinin ya yi Allah wadai da wani ƙazamin harin “ƴan ta’adda” a yayin wani taron siyasa a arewa maso yammacin Pakistan.

Fashewar wadda ta auku a lardin Khyber Pakhtunkhwa a yammacin ranar Lahadin da ta gabata ta kashe mutane 40 tare da jikkata sama da 150.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Iran ta fitar, kakakin ya miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnatin Pakistan da al’ummar ƙasar inda ya ƙara da cewa Iran na goyon bayan Pakistan sakamakon wannan mummunan lamari.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta kwaso ‘yan Najeriya 112 da suka maƙale daga ƙasar Libya

Fashewar ta auku ne a wani taron siyasa da aka gudanar a gundumar Bajaur, wanda ya tara membobi sama da 400 da magoya bayan jam’iyyar Jamiat Ulema-e-Islam-F (JUI-F).

Sai dai babu wanda ya ɗauki alhakin kai harin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...