Gwamna Buni ya nemi goyon bayan UNDP don daƙile barazanar sauyin yanayi

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya ce illar sauyin yanayi shi ne babban abin da ke damun gwamnatin jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da ya karɓi baƙuncin shugaban hukumar raya ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP) na shiyyar Arewa maso Gabas, Mista Moncef Kartas wanda ya kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati, Damaturu.

Gwamna Buni ya ce, jihar ta fuskanci ƙalubale daban-daban na shiga hamada da ambaliyar ruwa. Har ila yau, tana raguwa da girman sashinta zuwa mamaye hamada, da kuma yin babban asara ga ambaliyar ruwa na shekara.

KU KUMA KARANTA: Zan tallafa wa jami’an tsaro a jihar Yobe, don ci gaban ɗorewar tsaro a jihar – Gwamna Buni

Ya kuma yi ƙira ga hukumar ta UNDP a matsayinta na abokan hulɗa da su duba waɗannan bala’o’i guda biyu da nufin lalubo hanyoyin da za a bi wajen duba waɗannan baraza domin kare al’umma da hanyoyin rayuwarsu.

“A yayin da nake tabbatar muku da ƙudurinmu na wannan haɗin gwiwa, ina mai tabbatar muku da cewa gwamnatin jihar Yobe za ta ci gaba da sauƙe nauyin da ke wuyanta domin samun nasarar aiwatar da ƙawancen domin amfanin al’ummarmu,” in ji Gwamna Buni.

Ya yaba wa shugaban hukumar UNDP na shiyyar Arewa maso Gabas, Mista Moncef Kartas da tawagarsa bisa haɗin gwiwar da aka yi tsakanin UNDP, gwamnatin Japan da gwamnatin jihar Yobe, wajen farfaɗo da ayyukan sake gina al’ummar jihar, musamman waɗanda tashin hankalin ya shafa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *