’Yan bindiga sun sace Hakimi da manoma 2 a Kaduna

‘Yan bindiga sun yi barazanar auran matan da aka sace a Zamfara, sun buƙaci a ba su naira miliyan 12 (Bidiyo)

Wasu mata huɗu da aka yi garkuwa da su da suka haɗa da ɗalibar kwalejin fasaha da kimiyya ta jihar Zamfara da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su, sun tayar da ƙura kan barazanar da masu garkuwar ke yi na auran su idan iyayensu suka ka sa biyan kuɗin fansa naira miliyan 12.

Waɗanda aka sace, wanda aka kama a hanyar Birnin Magaji-Ƙaura Namoda watanni shida da suka gabata a lokacin da suke dawowa daga ɗaurin aure, sun bayyana hakan ne a cikin mintuna biyu da daƙiƙa 19 da jaridar News Point Nigeria ta samu ranar Asabar.

Waɗanda aka kama masu suna Ummukhair, Aisha Yahaya, Jamila Yahaya, da Ummu Sani sun kuma ce waɗanda suka sace su sun baiwa iyalansu mako guda domin su biya kuɗin fansa.

“Muna roƙonku iyaye da sunan Allah. Muna cikin matsala a nan tare da masu garkuwa da mu.

Don Allah a nemi kuɗi don ƙwato mana ’yancinmu,” in ji su.

“Gwamnatin da ta gabata ta Gwamna Bello Matawalle ta gaza wajen ganin an sako mu.

Wannan shi ne wata na shida da wasu kwanaki a cikin bauta. Muna roƙon gwamnatin Gwamna Dauda Lawal da ta yi wani abu.”

KU KUMA KARANTA: Ƴan bindiga sun kashe basarake sun ƙona gawarsa a Imo

Wani dattijo ga ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Aminu Yahaya ya shaidawa News Point Nigeria cewa an yi garkuwa da shida daga cikin ‘yan matan yayin da aka sako biyu daga cikinsu bayan an biya kuɗin fansa naira miliyan shida.

“Ni ne na karɓo musu sauran kuɗin fansa naira miliyan 6 kafin su sako ‘yan mata biyu,” ya ƙara da cewa.

“Yanzu sun ba mu wa’adin mako guda don biyan Naira miliyan 12 ko kuma su aurar da ‘yan uwanmu mata.”

Don haka ya yi ƙira ga gwamnatin jihar da ‘yan ƙasa da su kawo musu ɗauki.

Ku kalli bidiyon a nan:


Comments

One response to “‘Yan bindiga sun yi barazanar auran matan da aka sace a Zamfara, sun buƙaci a ba su naira miliyan 12 (Bidiyo)”

  1. […] KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun yi barazanar auran matan da aka sace a Zamfara, sun buƙaci a ba su naira miliyan… […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *