Daga Ibraheem El-Tafseer
Mamallakin kamfanin Twitter Elon Musk ya ce yana duba yiwuwar sauya wa shafin sabon tambari.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Elon Musk ya ce ”Nan ba da jimawa ba za mu sauya wa twitter tambari, ta hanyar musanya hoton tsuntsun da a yanzu ke mazaunin alamar shafin.
Ya ƙara da cewa za a sauya hoton tsuntun da alamar harafin ‘X’
Hamshaƙin ɗan kasuwar ya ce ya zaɓi sauya wa shafin tambarin ne domin tabbatar da shafin ya bambanta da kowanne.
KU KUMA KARANTA: Yadda za ka kare shafinka na Facebook da Twitter daga masu ƙwace
Elon Musk ya kuma bayar da samfurin misalin yadda sabon tambarin shafin zai kasance, ta hanyar wallafa bidiyon sabon tambarin a shafinsa.
A baya-bayan nan dai mai kamfanin Meta da ya mallaki shafin Facebook da Instagram da Whatsapp ya ƙaddamar da sabon shafin ‘Thread’ da ake kallo a matsayin kishiya ga shafin Twitter.
Shafin da ya samu miliyoyin mabiya a faɗin duniya.
[…] KU KUMA KARANTA: Zan sauya wa Twitter sabon tambari – Elon Musk […]