Connect with us

Labarai

Gwamna Zulum ya kai ziyarar bazata a asibitin Gwoza, ya yi takaicin ganin asibitin

Published

on

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya nuna damuwarsa kan rashin wutar lantarki da sauran yanayin da ya samu babban asibitin garin Gwoza ke ciki.

Gwamnan ya bayyana ɓacin ransa a lokacin da ya kai wa asibitin ziyarar ba-zata da tsakar daren ranar Asabar.

Cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa shafinsa na Twitter, ya ce ya kwana a garin wanda shi ne shalkwatar ƙaramar hukumar Gwoza da ke kudancin jihar.

A ziyarar Zulum ya kewaya sassan asibitin domin duba irin kayayyaki da yadda asibitin ke aiki.

KU KUMA KARANTA: El-Rufa’i ya rushe asibiti, makarantu da gidajen jama’a ƙasa da sati ɗaya ya bar mulki

A lokacin ziyarar gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda ya samu asibitin.

Ya ce ”Abin takaici ne halin da babban asibitin garin Gwoza ke ciki, babu manyan abubuwan buƙata a asibitin kamar wutar lantarki. Hakiƙa hakan zai kawo cikas da cutarwa ga marasa lafiyar da ke kwance a asibitin, tare da durƙusar da shirinmu na inganta asibitoncin jiharmu”.

Gwamnan ya kuma nuna ɓacin ransa kan rashin sanar da shi halin da asibitin ke ciki.

”Ba zan iya wanke kai na ko ƙaramar hukuma daga wannan laifi ba, dukkanmu mun gaza samar da abin da ake buƙata”.

Zulum ya kuma tabbatar wa da marasa lafiyar da ke kwance a asibitin cewa za a magance matsalolin da asibitin ke fuskanta, inda nan take ya bayar da umarnin fara gyara wuraren da suka lalace ciki har da wutar lantarkin asibitin.

Haka kuma gwamnan ya yaba wa ma’aikatan asibitin, waɗanda duk da rashin hali mai kyau da asibitin ke ciki ya same su a bakin aikinsu, inda ya alƙawarta saka mu da alkairi kan sadaukarwar da ya ce suna yi duk kuwa da tarin ƙalubalen da suke fuskanta.

Gwamna Zulum ya saba kai irin wannan ziyara ta ba-zata zuwa makarantu a asibitoci a faɗin jihar, a wani yunƙurin na sanin haƙiƙanin halin da suke ciki.

2 Comments

2 Comments

  1. Pingback: Gwamna Zulum ya ba da umarnin gyaran asibitoci biyu da makaranta a Baga | Neptune Prime Hausa

  2. Pingback: Ma’aikatar lafiya a jihar Neja, ta rufe wasu asibitoci masu zaman kansu a jihar | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like