Connect with us

Al'ajabi

Bayan kwana uku da binne shi, an tono shi, an same shi da ransa

Published

on

A shekara ta Alif da Ɗari Tara da Talatin da Bakwai (1937), an ayyana Angelo Hays, ɗan ƙasar Faransa da ya mutu kuma aka binne shi bayan kwana uku.

Bayan kwana biyu, binciken inshora ya tono shi kuma ya same shi a sume, daga baya ya warke sarai kuma ya ci gaba da rayuwa har zuwa tsawon shekaru Casa’in a duniya.

Daga baya, Hays ya ƙirƙiri akwatin gawa, kabad ɗin ajiye kayan abinci, sinadarin tsaftace banɗaki, ɗakin karatu, da na’urar sadarwar Rediyo.

Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Wata mata ta binne jaririn da ta haifa da rai a cikin daji | Neptune Prime Hausa

Leave a Reply

Al'ajabi

Matashi ya koma rayuwa a cikin kogon bishiya a Yobe

Published

on

Matashi ya koma rayuwa a cikin kogon bishiya a Yobe

Matashi ya koma rayuwa a cikin kogon bishiya a Yobe

Daga Ibraheem El-Tafseer 

Wani matashi mai suna Muhammadu mazaunin wani ƙauye kusa da ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe, ya haƙura da rayuwa cikin garinsu, ya koma rayuwa cikin kogon wata bishiyar Kuka, yau kimanin shekaru biyar yana rayuwa a cikinta, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Wakilin Neptune Prime Hausa ya tuntuɓi wani mazaunin garin Fika, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da labarin.

Inda ya ce Muhammadu ya shaida wa mazauna yankin cewa, dalilansa da suka saka ya koma rayuwa cikin kogon bishiyar Kuka shi ne, Allah ya yi masa wata baiwa ta sanin abubuwan da za su iya faruwa cikin kwanaki ko watanni masu zuwa a cikin yawan mafarke-mafarken da yake yi, amma idan ya sanar da mutanen garinsu sai su yi masa kallon mahaukaci.

Kullum idan ya ba su labarin wani al’amuran da za su faru sai ‘yan ƙauyen su ɗauke shi marar hankali, hakan sai ta sa ya ji ba zai iya zama cikin su ba, sai ya koma cikin kogon bishiyar Kuka wanda yanzu haka ya yi tsawon shekaru biyar yana kwana a cikinta.

 

Za a ji ƙarin bayani a rahoton mu na gaba.

Continue Reading

Al'ajabi

An watsa wa budurwa tafasasshen man gyaɗa a fuska a Zariya

Published

on

An watsa wa budurwa tafasasshen man gyaɗa a fuska a Zariya

An watsa wa budurwa tafasasshen man gyaɗa a fuska a Zariya

Daga Idris Umar, Zariya

Wani abin tausayi da ban al’ajabi da ya faru birnin Zariyan jihar Kaduna, inda aka wayi gari da mummunan labarin yadda aka watsa wa wata budurwa tafasasshen man gyaɗa a fuska.

Ita wannan budurwa mai suna Husaina, wadda ke unguwar layin Tanimu Ƙaya, Hayin Dogo, Samaru, a cikin garin Zariya.

Murhun da Husaina ke soya awara

Yadda abin ya faru shi ne, Husaina tana gaban sana’arta ta suyar Awara, wani yaro mai suna Suleiman Abubakar ya zo ya ja ta da cacar baki har ta kai ga zagin mahaifiyarta, ita kuma da ta ji zafi ta rama. Bayan ta rama ne, sai wannan matashi ya sanya ƙafa ya harba mata tafasasshen man da ke kan wutar da take soya Awaran a wannan lokacin.

Nafisa Ibrahim yayar Husaina Ibrahim wacce aka ƙona.

Hakan ya sa nan take fuskarta ta ƙone gaba ɗaya haɗe da wasu sassa na jikinta. Inda nan take kamanninta suka canza kamar ba ita ba.

Ibrahim Ibrahim, wanda ya fara yaɗa lamarin a social media, mazaunin garin samaru

Bayan faruwar lamarin, jama’a suka yi iya bakin ƙoƙarinsu suka damƙe matashin, inda suka miƙa shi ga hukumar tsaro na farin kaya don gudanar da bicike.

Wakilin Neptune Hausa, Idris Umar tare da mai unguwa malam Ibrahim Hasan ( kakale)

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama matar da ta kwara wa mijinta tafasasshen man gyaɗa ta kwaɗa masa guduma ta gudu

Wakilinmu ya ziyarci gidan su Husaina don jin haƙiƙanin abin da ya faru, da kuma ganewa idonsa yadda jikin nata ya ke.

Husaina babu wani kulawa da take samu ta ɓangaren shan ingantattun magunguna don ta samu lafiya mai inganci.

Aliyu Ibrahim mazaunin unguwar da lamarin ya faru tare da wakilin Neptune Prime Hausa

Wakilinmu ya tambayi wasu daga cikin ‘yan’uwanta akan me ya sa aka barta a gida duk da irin halin da take ciki na irin wannan jinya mai buƙatar kulawa ta musamman?

Sai wata daga cikin danginta ta ce, “Wallahi ba wata hanya da za a kaita Asibiti, domin yanzu haka mahaifinmu ma shi ma ba shi da ƙoshin lafiya, ita ce kaɗai take kula da gidan namu, kuma ga wannan bala’in ya faɗo mata sai dai in akwai wanda zai taimaka mana don Allah to” inji ta.

Gidan iyayen Husaina

Husaina dai ‘yar talakawa ce, hasalima da ‘yar wannan sana’arta ta, ta Awara take ciyar da gidan nasu, ga shi yanzu kuma ita ma tana kwance. Hatta kuɗin da za a kai ta Asibiti ma babu, ballantana na abinci. Husaina dai na buƙatar taimako sosai daga al’umma.

Jama’a dai sun zura ido, suna jira su ga wane irin hukunci hukuma za ta yanke wa wannan yaro.

 

Continue Reading

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

You May Like