Gwamnan Yobe ya gana da sakataran gwamnatin tarayya don samar da ayyukan ci gaba a jihar

1
304

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, ya ziyarci sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, domin tattaunawa kan ci gaban jihar da kuma wasu ɓangarorin haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya.

Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Gwamna Buni kan harkokin yaɗa labarai, Mamman Mohammed, ya rabawa manema labarai a Damaturu.

Buni ya bayyana yanayin ayyukan gwamnatin tarayya a jihar da kuma buƙatar gaggawar shiga tsakani da gwamnatin tarayya.

Idan dai za a iya tunawa dai a bara ne ambaliyar ruwa ta tafi da wasu titunan gwamnatin tarayya a jihar.

KU KUMA KARANTA: Ƙananan Hukumomi uku na Yobe suna kashe miliyan 299.1 a ayyuka

Sauran ayyukan sun haɗa da samar da ruwan sha na yankin Damaturu, aikin ruwan Fika, samar da wutar lantarki da sauransu.

Sakataren gwamnatin tarayya Sanata Akume ya tabbatarwa Gwamna Buni cewa gwamnatin tarayya za ta duba waɗannan ayyuka domin inganta rayuwar al’umma.

Ya kuma ba da tabbacin gwamnatin Tinubu na yin aiki a kafa ɗaya domin amfanin al’ummar jihar.

Hakazalika, Gwamna Buni ya gana da masu saka hannun jari masu zaman kansu tare da ba da shawarar kafa masana’antun haɗin gwiwar noma a jihar.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar Yobe za ta kafa ƙauyen masana’antu domin samar da kayayyakin da za su jawo hankalin masu zuba jari a jihar.

1 COMMENT

Leave a Reply