Hukumar DSS ta saki tsohon Gwamnan Zamfara, Yari

0
271

Daga Ibraheem El-Tafseer

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta saki tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari, bayan amsa tambayoyin Naira Biliyan 45 na zaɓen tsohon shugaban Najeriya Buhari.

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya samun ‘yancinsa biyo bayan tsare shi da jami’an ‘yan sandan sirri na Najeriya, DSS suka yi a makon da ya gabata.

Neptune Hausa ta samu labarin a safiyar yau Lahadi cewa Yari ya fita daga tsarewar da Hukumar ta DSS take masa a daren jiya Asabar.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda a Zamfara sun bi umarnin kotu, sun mayar wa da tsohon gwamna motocin sa

Jaridar Sahara Reporters ta rawaito cewa hukumar DSS ta tsare tsohon gwamnan kuma Sanata mai ci, Abdul’Azeez Yari kan kuɗi sama da naira biliyan 45 da aka fitar a zamanin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Leave a Reply