Gaskiyar abin da ya faru game da matar da ta kashe mijinta a Bauchi.

0
291

Daga Ibraheem El-Tafseer

Hukumar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta tabbatar da labarin kisan da maimunatu ta yi kisan gilla ga mijinta mai suna Aliyu Mohammad.

Maimunatu Sulaiman ‘yar shekara 21 a duniya da ke zaune a unguwar ƙofar Dumi a ƙwaryar Bauchi ta kashe mijinta, Aliyu Mohammad sakamakon rashin jituwar da ta ɓarke a tsakaninsu.

Majiya daga yankin ta bayyana cewa an samu rashin jituwa ne a tsakanin miji da matar, sakamakon yunƙurin da mijin ya yi na ƙara aure.

A wani ruwayar kuma ance mijin nata yana mata faɗa ne kan fita yawo da take yi.

Bayan samun husuma cikin dare tsakanin su matar ta ɗauki wuƙa ta daddaɓa wa mijin wuƙa ne a ƙirjinsa da gefen cikin sa wajajen da ake ƙira da makasa wanda hakan ya yi sanadin ajalinsa.

Hakan ya faru ne a ranar 5 ga watan Yulin 2023 a unguwar Ƙofar Dumi. Yanda wasu suka sheda mana cewa wuƙar ma ta karɓi aron tane!

KU KUMA KARANTA: An tsinci jariri da ransa, bayan sa’o’i 24 da kashe mahaifiyarsa

Yanzu haka dai rundunar ‘yan sandan jihar, ta ce sun cafke matar da ake zargi da kisan kan.

A sanarwa da kakakin ‘yan sandan jihar, Bauchi ASP Aminu Gimba Ahmed ya fitar a ranar Juma’a ta ce, “A ranar 5 ga watan Yuli 2023 jami’an caji ofis ɗin ‘yan sanda da ke Township, Bauchi sun kama wata Maimunatu Sulaiman kan zargin aikata kisan kai.

“Lokacin da jami’an suka samu rahoton faruwar lamarin, sun garzaya zuwa inda lamarin ya faru tare da ɗaukar wanda lamarin ya rutsa da shi da ita kanta wadda ake zargi zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Bauchi.

“Amma likitoci sun tabbatar da mutuwar mijin sakamakon rauni da ya samu a ƙirjinsa, yayin da ita kuma wadda ake zargin ta samu wasu raunuka a cikinta.” da ake zargin ta yanka kanta ne domin ɓat da sawu da za’a iya zaton hari aka kai musu su duka.

Binciken ‘yan sanda ya nuna cewa wadda ake zargin ta soki mijinta a ƙirjinsa sakamakon rashin jituwar da ta ɓarke a tsakaninsu.

Wadda ake zargin ta amsa laifin da ake tuhumarta da shi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Auwal Musa Mohammad, ya umarci mayar da binciken lamarin zuwa sashen kula da manyan laifuka (SCID) don zurfafa bincike.

Leave a Reply