Yanayin zafi a Saudiyya ya kai kashi 50

1
321

Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun shawarci mahajjata da su yi sallar Juma’a a masallatai mafi kusa, saboda yanayin zafi a ƙasar.

Hukumar kula da yanayi ta ƙasar Saudiyya, (SAMA), a ranar Alhamis ta bayyana cewa yanayi zai kai maki 50 a ranar Juma’a 7 ga watan Yuli.

Dokta Ibrahim Sodangi, kodinetan Makkah na Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.

“Saboda haka, gwamnatin Saudiyya ta shawarci alhazai da su gudanar da Sallar Juma’a a masallatan da ke kusa da su domin kada su shiga cikin yanayi mai tsanani.

“Don haka an umurci Alhazan Najeriya da su bi wannan umarni,” in ji Sodangi.

1 COMMENT

Leave a Reply