Auren nan mai ban sha’awa na tsohuwar jarumar Kannywood, Wasila Isma’il, da darakta kuma jarumi Al-Amin Ciroma, ya mutu, kamar yadda mujallar Fim ta wallafa a yau.
Tun a kwanan baya mu ke jin ana ta raɗe-raɗin mutuwar auren, amma sai mu ka ɗauka irin ji-ta-ji-tar nan ce da aka saba yaɗawa game da ‘yan fim.
Amma a yanzu mujallar Fim ta tabbatar da mutuwar auren bayan wakilan mu sun tattauna da makusantan ma’auratan waɗanda suka tabbatar mana da sahihancin labarin.
Tsegumi a kan rubuwar auren dai ya faro ne daga yadda wasu suka gano Hajiya Wasila ta cire kalmar ‘Misis Ciroma’ daga sunan ta kamar yadda ta saba yi a duk wani rubutu da za ta yi, sai aka ga ta mayar da sunan ta ‘Wasila Isma’il’ kawai. Mutane sun yi ta neman dalilin hakan.
KU KUMA KARANTA: Yadda mutuwar Alhaji Mala na shirin ‘Daɗin Kowa’ ta jijjiga Kannywood
Majiya ƙwaƙƙwara ta tabbatar wa da mujallar Fim cewa mutuwar auren ya faru ne kimanin watanni biyu da suka gabata. “A yanzu ko dai ta kammala idda ko dai ta na gab da kammalawa,” inji wani bakin da ba ya ƙarya.
Majiyar tamu ta ce wani abu kuma wanda ya saɓa a iya gane mutuwar auren farat ɗaya ba shi ne saboda bisa al’adar mu da zarar aure ya mutu sai a ga mace ta kwashe kayan ta daga gidan miji, to amma ita Wasila tun da su ka rabu a gidan auren ta ke zaune tare da ‘ya’yan ta, ba ta tashi ba.
Masu ba mu labarin ba su bayyana takamaiman dalilin mutuwar auren ba.
Wakilan mu sun tuntuɓi Wasila da Malam Al-Amin kan wannan al’amari maras daɗi da ya faru a tsakanin su, to amma ba wanda ya yarda ya yi bayani.
Auren Wasila da Al-Amin ya na ɗaya daga cikin aurarrakin ‘yan Kannywood da ake kafa misali da su na zaman da ya daɗe sosai, har da ƙaruwar ‘ya’ya. ‘Ya’ya biyar Wasila ta haifa masa, mata uku, maza biyu, amma ɗaya ya rasu.
Idan kun tuna, a ranar Alhamis, 6 ga Oktoba, 2022 Al-Amin Ciroma da Wasila sun yi bikin cikar su shekara 20 da aure, wanda hakan ya jawo masu addu’ar fatan alheri da roƙon Allah ya ƙaro shekaru masu yawa nan gaba.
Tun wajen ƙarfe 10:00 na safe a ranar, daraktan ya wallafa wata fosta mai ɗauke da hoton sa da iyalin sa gaba ɗaya a soshiyal midiya, kuma ya yi wani rubutu kamar haka: “Our 20th Wedding Anniversary,” sannan ya wannan lissafin: “Watanni 240, makwanni 1,043, kwanaki 1, 306, sa’o’i 176, 344, mintuna 10, 520, 640, saƙwanni 631, 238, 400, ‘ya’ya biyar, ɗaya ya rasu, Allah ya jiƙan Muhammad Al-Baƙir, amin.”
Haka kuma a dai wannan ranar, mujallar Fim ta buga hirar musamman da ta yi da Ciroma ɗin, inda ya bayyana sirrin ɗorewar auren nasu.
Ya ce, “Alhamdulillah. Shekara ashirin a zaman aure ana tare, sai dai hamdala. Ka san rayuwar aure rayuwar addini ce, kamar yadda kowa ya sani. Tilas ne mutum ya jajirce, ya kuma yi haƙuri da duk jarabawan da zai ci karo da su na zaman taren, musamman a yanzu ma da riƙon auren ya ke da tsada a ƙasar Hausa. Galibi, za ka iske da dama cikin aurarrakin yanzu suna saurin rugujewa saboda matsaloli daban-daban na haɗakar zamantakewa.
“To, ka ga kenan, duk wanda Allah ya raya shi har ya shafe shekaru irin wannan ana tare, shakka babu, tilas ka yi godiya a gare shi.”
Ciroma, wanda shi ne kuma kakakin Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar masu shirya Fina-finai ta Nijeriya (MOPPAN), ya yi tsokaci kan masu ‘yan fim ba su daɗewa a aure, ya ce, “Auren ‘yan fim shi ma wata makaranta ce ta daban. Baya ga sa ido da mutanen gari ke yi mana, akwai yadda kuma ake kallon mu. Ana saurin nuna cewa matan fim ba sa zama a gidajen su na aure. Hakan ne ma ya sa ake yi masu kuɗin goron.
“Amma kuma da hikimar Allah, sai mu mu ka tsallake duk waɗannan maganganun.”
Ya bayyana wani abu wanda ba kowa ya sani ba, ya ce: “Ba na tsammanin akwai wata ‘yar fim da su ka yi aure tare da Wasila wadda ta kai ta daɗewa ba tare da wani rikici ko ce-ce-ku-ce ba.
“Don haka na ke yin ƙira ga sauran ‘yan’uwa da abokan arziƙi a cikin masana’antar Kannywood da mu ci gaba da ba maraɗa kunya, mu jajirce mu riƙe wa juna amana.”
Abin ikon Allah, sai ga shi su ma sun faɗa cikin wannan rami da wasu suka faɗa.
Shakka babu, wannan mutuwar auren za ta ba mutane mamaki matuƙa, kamar irin mutuwar auren jaruma Mansurah Isah da jarumi kuma mawaƙi Sani Musa Danja da mujallar Fim ta fara bayyana faruwar sa a ranar 27 ga Mayu, 2021.
Sai dai kamar yadda wani daga cikin su ya faɗa wa mujallar Fim, “Allah ya sa hakan shi ya fi alheri.”
Idan da rabon komawa kuma, mu na addu’ar Allah ya sasanta tsakanin su, amin.