No menu items!

Sample Page Title

Date:

An gano wani jinjiri ɗan wata bakwai mai suna Habibu da ransa sa’o’i 24 bayan wasu ‘yan bindiga sun harbe mahaifiyarsa har lahira a hanyar Pandogari zuwa Allawa a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a jajibirin sallar Eid el-Kabir. An samu jaririn ne cikin al’ajabi, jinjirin yana barci a bayan rasuwar mahaifiyarsa da sa’o’i 24.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ‘yan bindigar da suka tare hanyar Pandogari zuwa Allawa sun harbe fasinjoji shida, ciki har da wata ɗalibar SS 2 na Kwalejin Kimiyyar Mata ta Maryam Babangida da ke Minna, mai suna Hauwa Aliyu da kuma mahaifiyar jaririn.

KU KUMA KARANTA: Mayaƙan Al-Shabaab sun kashe wasu ƙauyawa biyar a yankin gaɓar tekun Kenya

Shugaban majalisar matasan Lakpma, Jibril Allawa, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ‘yan banga na yankin ne suka ceto yaron.

Ya ce, “Abin mamaki, jaririn na ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira daga harin da aka kashe mutane shida.

‘Yan banga da suka je washegarin kwashe gawarwakin waɗanda abin ya shafa sun gano jaririn yana barci a bayan mahaifiyarsa da ta mutu”.

“Lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Yuni, kuma mutane shida sun rasa rayukansu.

Maryam ta ƙira ta sanar mana za ta zo gida don yin Sallah. Muka ce mata ta koma makaranta ta yi bikin Sallah a can amma ta dage cewa tana son ta zo gida mu yi biki.

“Wani Abubakar Ismail, ɗan shekara 16, wanda ya samu raunin harbin bindiga a ƙirjin sa, ya yi nasarar gudu daga nesa kafin a ceto shi, kuma yanzu haka yana samun kulawa a asibiti,” ya ƙara da cewa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

2 COMMENTS

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...