Mutane biyar sun mutu yayin da wani jirgin ruwa ya kife a Kalaba

0
232

An yi fargabar mutuwar mutane biyar a ranar asabar bayan da wani jirgin ruwa mai sauri ya kife a mashigin ruwan Kalaba.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya bayar da rahoton cewa, jirgin ya kife ne a hanyarsa ta zuwa Oron a Akwa Ibom.

Wani babban jami’in sojan ruwa da ke aiki da rundunar sojojin ruwa ta Gabashin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce rundunar ta taka rawar gani wajen ceto wasu daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su.

“Rundunar sojin ruwa sun shiga aikin ceto; a ƙalla mun ceto 14 daga cikinsu.

KU KUMA KARANTA: Mutane huɗu sun mutu, da dama sun jikkata a hatsarin mota a hanyar Ibadan

“Ba zan iya ba ku ainihin matsayin jirgin ba saboda kawai mun garzaya ne don aikin ceto, amma na tabbata nan ba da jimawa ba rundunar za ta fitar da wata sanarwa kan hakan,” in ji shi.

NAN ta tattaro cewa mutane 20 ne suka shiga jirgin a Marina a Kalaba.

Duk da haka, ya kife da mintuna bayan ya tashi daga filin jirgin ruwa na Kalaba Marina.

Leave a Reply