NDLEA ta kama ƙwayoyin Tramol da Exol-5 a jihohi uku na arewa

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta kama wasu ƙwayoyin Tramadol da suka kai 122,900 da Exol-5 a jihohin Bauchi, Kano da Benue.

Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, inda ya ce an gano ƙwayoyin Tramadol dubu 87,000 daga hannun wani da ake zargi, Tony Ogbonna, mai shekaru 40, a unguwar Yelwa da ke Bauchi, a ranar 17 ga watan Yuni.

Mista Babafemi ya ƙara da cewa, ƙwayoyin tramadol dubu 13,800 da wani da ake zargi ya yi watsi da su zuwa Geidam a Yobe, an kuma gano su a filin shaƙatawa na ‘Yankaba a Kano, a ranar 14 ga watan Yuni.

KU KUMA KARANTA: NDLEA ta bankaɗo ɗakin da ake haɗa sinadaran ƙwayar meth, ta ƙwato fakitin haramtattun ƙwayoyi da dama

Mista Babafemi ya ce a wannan rana a Benue, an kama wani da ake zargi, Chidera Gabriel da ƙwayoyi guda dubu 22,100 na maganin ‘opioid’ a wani wurin duba lafiyar NDLEA a Vandeikya.

Kakakin hukumar ta NDLEA ya bayyana cewa jami’an hukumar a Kaduna sun kama wata mata mai suna Pharmacist Ikwebe Ori.

Mista Babafemi ya ce kamen ya biyo bayan yunƙurin da ta yi na yin amfani da takardun jabu wajen siya tare da rarraba kwali shida na allurar pentazocine tare da kwalabe guda dubu 2,000.

“Ta yi iƙirari cewa ta yi amfani da takardun ƙarya na wani asibitin Kaduna wajen ba da odar maganin, wanda ta shirya rarrabawa a Kaduna, Abuja da Sokoto.

“Da farko an kama kayan ne a reshen filin jirgin sama na Murtala Muhammed International Airport (MMIA), Ikeja yayin da wani jami’in sufuri ya tura shi Kaduna,” inji shi.

Hakazalika, jami’an hukumar NDLEA a Jamhuriyar Nijar sun kama jimillar tabar wiwi kilogiram dubu 1,072 a samame guda biyu. Babafemi ya ce an gano kilogram ɗari 726 na haramtattun kayan a gidan man Oyoyo da ke kan titin Kaduna zuwa Abuja a ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni.

“Mutane huɗu da ake zargi: Aminu Mohammed, 50; Nasiru Mohammed, 30; Rabiu Haruna mai shekaru 29 da Hamza Abubakar mai shekaru 18 an kama su.”

A cewarsa, a ranar 16 ga watan Yuni, jami’an tsaro sun kama wata mota ƙirar Mercedes 1422 mai lamba MKD 116 ZM a kan hanyarta daga Umunede jihar Delta ɗauke da galan na dabino da za a kai a kasuwar Garki da ke Abuja.

“Duk da haka, direban babbar motar mai suna Jekwe Udenze, mai shekaru 38, tare da mataimakansa guda biyu: Gabriel Nzekwube, mai shekaru 43, da Chima Uzoma, mai shekaru 42, sun tsaya a Uromi, Edo.

“Sun kwashe buhunan tabar wiwi guda 19 mai nauyin kilogiram 346, inda za a kai su a Dumez Luxury Park da ke kan titin Kaduna, Suleja ga wani Ignatius Mokwe mai shekaru 47.

“An kama direban da mataimakansa biyu da kuma mai haramtaccen kayan, Ignatius Mokwe,” in ji shi.


Comments

One response to “NDLEA ta kama ƙwayoyin Tramol da Exol-5 a jihohi uku na arewa”

  1. […] KU KUMA KARANTA: NDLEA ta kama ƙwayoyin Tramol da Exol-5 a jihohi uku na arewa […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *