‘Yan sanda a Zamfara sun bi umarnin kotu, sun mayar wa da tsohon gwamna motocin sa

1
252

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara a ranar Asabar ɗin da ta gabata ta ce ta mayar da dukkan motocin da ta kama daga hannun tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya faruwar lamarin a ranar Asabar ta hanyar tattaunawa ta wayar tarho.

Abubakar ya ce an mayar da motocin ne bisa bin umarnin babbar kotun tarayya da ke Gusau.

Kotun ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Aminu Bappah-Aliyu, ta bayar da umarnin a ranar 15 ga watan Yuni, ta umurci dukkanin hukumomin tsaron da suka kwashe motocin da ke gidajen Matawalle da ke Gusau da Maradun, da su mayar da su cikin sa’o’i 48.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Zamfara ta bai wa Matawalle wa’adin mayar da motocin alfarma na biliyoyin nairori

NAN ta ruwaito cewa jami’an tsaro sun kwashe motocin daga gidajen biyu bisa umarnin gwamnatin jihar. Kotun ta bai wa duk wanda ke da hannu a harin da aka kai wa gidajen tsohon gwamnan wa’adin sa’o’i 48 domin su bi wannan umarni.

“Eh, rundunar ‘yan sanda ta bi umarnin kotu dangane da mayar da dukkan motocin tsohon gwamna Bello Matawalle.

“Mun mayar da dukkan motocin zuwa harabar babbar kotun tarayya da ke Gusau, kamar yadda nake magana da ku a yanzu, babu wata mota guda da ke hannun ‘yan sanda,” in ji Abubakar.

Kotun ta kuma bayar da umarnin dakatar da waɗanda ake ƙara a ƙarar da Matawalle ya shigar a gaban kotu daga ɗaukar wani mataki na gaba dangane da lamarin.

Waɗanda suka amsa sun haɗa da Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya da kuma kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara.

Sauran sun haɗa da hukumar tsaro ta farin kaya, (SSS), da kuma jami’an tsaron farin kaya na Najeriya, (NSCDC). Kotun ta kuma umarci jami’an tsaro da su nesanta kansu daga duk wani mataki da za a ɗauka, har zuwa lokacin da za a saurari ƙarar da kuma yanke hukunci a gabanta.

Suleiman Idris, mai magana da yawun Gwamna Dauda Lawal na Zamfara, ya ce an ƙwato fiye da motoci 40 a gidajen tsohon gwamnan guda biyu.

Ya kuma tabbatar da cewa hukumomin tsaro sun ɗauki matakin ne bisa umarnin gwamnatin jihar.

1 COMMENT

Leave a Reply