Mutane huɗu sun mutu, da dama sun jikkata a hatsarin mota a hanyar Ibadan

4
323

Mutane huɗu ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hatsarin mota da ya auku a babbar hanyar Ibadan zuwa Oyo a ranar Asabar.

Wasu da dama kuma sun jikkata a cikin motar bas da hatsarin ya rutsa da su yayin da ta yi taho mu gama da su.

Kwamandan rundunar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) a Atiba, Oyo, DCC Bayode Olugbesan, ya ɗora alhakin hatsarin da gudun wuce gona da iri.

Mista Olugbesan ya ce motar bas mai mutane 14 tana ɗauke da mutane 20 a lokacin da hatsarin ya auku.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya ba da umarnin a yi bincike kan hatsarin jirgin ruwa a Kwara

Ya ce an ajiye gawarwakin waɗanda suka mutu a ɗakin ajiyar gawa na asibitin jihar da ke Oyo.

“Bas ɗin, ɗauke da dukkan fasinjoji maza na tafiya zuwa yankin arewacin ƙasar lokacin da hatsarin ya auku,” in ji shi.

“An tsara bas ɗin don ɗaukar fasinjoji 14, amma an yi lodin fasinjoji 20,” in ji shi.

Mista Olugbesan ya yi ƙira ga masu amfani da hanyar da su yi taka tsantsan yayin tuƙi, da kuma gudun wuce gona da iri da kuma tafiye-tafiyen dare.

4 COMMENTS

Leave a Reply