Gwamnan Kano Abba, ya naɗa mataimaka 14

1
370

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da naɗin muƙamai guda 14.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran sa, Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Alhamis a Kano.

A cewar sanarwar, an naɗa Dakta Sani Ɗanjuma a matsayin babban mataimaki na musamman, (SSA), harkokin mulki; Bello Nuhu Bello, SSA na gudanarwa; Najeeb Bashir Nasidi, SSA na harkokin cikin gida; Dakta Abdurraman Kirare, SSA na harkokin cikin gida II da Safwan Garba, SSA ayyuka na musamman.

Sauran su ne Abdulƙadir Balarabe Kankarofi, SSA Protocol I; Salisu Yahaya Hotoro, SSA na kafafen yaɗa labarai na zamani; Mataimaki na Musamman, SA, Salisu Muhammad Kosawa; SA Social Media da Zulaihat Yusuf Aji, SA
mai ba da shawara na musamman kan Kafofin Watsa Labarai.
Rasheedat Usman, SA Secretariat, Personal Assistants, PAs, Ahmad Aminu Yusuf, PA Domestic, Ahmad Muhammad Gandu, PA Videography,  Isa Muhammad Giginyu, PA Photography da  Hassan Kabir, PA Social Media.

Sanarwar ta ce dukkan naɗe-naɗen sun fara aiki nan take.

1 COMMENT

Leave a Reply