NURTW ta goyi bayan shugaba Tinubu kan cire tallafin man fetur

Ƙungiyar ma’aikatan zirga-zirgar ababen hawa ta ƙasa (NURTW), ta yi alƙawarin bayar da cikakken goyon baya ga shirye-shirye da manufofin gwamnatin shugaba Bola Tinubu, a ƙoƙarinta na inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

Shugaban ƙungiyar, Tajudeen Baruwa ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga shugabannin shiyyar na ƙungiyar da suka kai masa ziyarar haɗin kai, ranar Alhamis a Abuja.

Shugabannin shiyyar NURTW sun kaɗa ƙuri’ar amincewa da shugabancin Baruwa tare da yin alƙawarin goyon bayan takararsa na shugaban ƙungiyar a karo na biyu.

Shugaban NURTW ya samu wakilcin mataimakinsa na musamman kan hulɗar ƙwadago da masana’antu Abuul Boga.

KU KUMA KARANTA: Cire tallafin mai: Za mu sakawa ‘yan Najeriya da manyan ayyukan jin daɗin rayuwa – Tinubu

Baruwa ya ce ƙungiyar ta yi imanin cewa cire tallafin man fetur zai sa a samu ƙarin kuɗaɗe domin raya ƙasa, ciki har da sake gina titunan ƙasar nan da suka lalace.

Sai dai ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da bayar da goyon bayan ƙungiyoyin ƙwadagon da ke buƙatar gwamnati don inganta tasirin cire tallafin man fetur ga ‘yan Najeriya.

Shugaban NURTW ya kuma jaddada buƙatar gwamnatocin jihohi musamman gwamnonin Kudu maso Yamma da su sake duba yadda za su maye gurbin NURTW da kwamitocin kula da wuraren shaƙatawa da garaje, PGMC.

Ya ci gaba da cewa ƙungiyar ta kasance ƙungiya ɗaya tilo da ta yi rijista ga direbobin kasuwanci a Najeriya.

“Saboda haka, muna so mu bayyana sarai, cewa kwamitin kula da wuraren shaƙatawa da garaji ba ƙungiyar ƙwadago ba ce da wata dokar ƙwadago ta sani a Najeriya.

“Ayyukan da suke yi ba bisa ƙa’ida ba ne kawai, har ma da ƙwace ayyukan ƙungiyar (NURTW).

“An shawarci ‘yan ƙungiyar da ke yankin Kudu maso Yamma da su rungumi ƙungiyar NURTW wadda ita ce ƙungiya ɗaya tilo da ta yi rajista kuma aka amince da ita ga duk direbobin ‘yan kasuwa a Najeriya.

“Hakazalika muna ƙira ga mutanen kudu maso yamma masu kishin ƙasa da su shiga tsakani, su kuma shawarci gwamnatocin jihohin da suka maye gurbin NURTW da PGMC, da su sake tunani.

“Muna ƙira gare su da su ƙyale ayyukan ƙungiyar a wuraren ajiye motoci da gareji daban-daban kamar yadda ake yi a wasu sassan ƙasar nan,” in ji shi.

Baruwa ya ƙara jaddada ƙudirinsa na kyautata rayuwar ‘ya’yan ƙungiyar, inda ya ƙara da cewa, shugabanni ya ƙaddamar da ƙarin kashi 100 na albashin ma’aikata da ƙarin girma ga ma’aikata da nufin ƙarfafa musu gwiwa.

Ya kuma ce ƙungiyar ta sake gyara babbar sakatariyar ƙasa da ta lalace zuwa matsayin ƙasa da ƙasa, wadda aka yi mata cikakkiya da na’urorin zamani. A cewarsa, hakan ya kasance don tabbatar da kyakkyawan yanayi ga jami’ai da ma’aikatan ƙungiyar.

“An samu ƙarin kashi 100 cikin 100 na alawus-alawus na ‘yan majalisar gudanarwa na ƙasa, shugabannin shiyyar, sakatarorin shiyya, sakatarorin jiha da ma’ajin jiha waɗanda su ma membobin majalisar zartarwa ne ta ƙasa ne.

“Za mu ci gaba da tabbatar da cewa ma’aikatanmu suna da ƙwarin gwiwa don samar da ayyukan yi da kuma ba su damar gudanar da aikin ƙungiyar,” in ji Baruwa.

Shugabannin shiyyar sun kaɗa ƙuri’ar amincewa da shugabancin ƙungiyar ta NURTW na ƙasa tare da yin alƙawarin goyon bayan zaɓen Baruwa a karo na biyu a matsayin shugaban ƙungiyar.


Comments

One response to “NURTW ta goyi bayan shugaba Tinubu kan cire tallafin man fetur”

  1. […] KU KUMA KARANTA: NURTW ta goyi bayan shugaba Tinubu kan cire tallafin man fetur […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *