Tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya sauka daga kujerarsa ta ɗan majalisar wakilan Najeriya, domin fara aiki a sabon muƙaminsa na shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa.
Sabon kakakin majalisar Tajudeen Abbas ne ya karanto wasiƙar murabus ɗin nasa a zauren majalisar ranar Laraba.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ne ya naɗa Gbajabiamila a matsayin sabon shugaban ma’aikata na fadarsa.
Femi dai ya samu nasara a zaɓen kujerar ɗan majalisar wakilan ƙasar mai wakiltar mazaɓar Surulere ta ɗaya a jihar Legas.
KU KUMA KARANTA: Mambobin ASUU su kwantar da hankalin su kan batun albashi – Gbajabiamila
An dai yi ta nuna damuwa kan yadda ɗan majalisar zai tafiyar da muƙaman biyu, bayan da ya ƙarbi rantsuwa tare da sauran ‘yan majalisar sabuwar majalisa ta 10 ranar Talata, har ma ya jefa ƙuri’arsa a zaɓen shugabannin majalisar.
A yanzu hukumar zaɓen ƙasar za ta shirya zaɓen cike-giɓi na ɗan majalisar wakilan mazaɓarsa.