Jirgin ruwa ɗauke da mutane sama da 100 ya kife a jihar Kwara

1
291

Wani jirgin ruwa ɗauke da mutane sama da 100 ya kife a kogin Neja da ke kusa da Patigi a jihar Kwara.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Talata a lokacin da suke komawa ƙauyen Ebbu bayan wani ɗaurin aure a unguwar Gboti.

Wani mazaunin Patigi, Malam Isah Gimba, ya ce kawo yanzu an gano gawarwakin mutane 15 daga cikin sama da 100 da ke cikin jirgin.

Sakataren ƙaramar hukumar Patigi, Malam Idris Mohammed, ya ce majalisar ta tara jama’a domin tallafa wa waɗanda suka tsira da rayukansu a faɗin Zakkan a Kwara da kuma ƙauyen Sanpi da ke maƙwabtaka da Kogi.

KU KUMA KARANTA: Mutane 18 sun mutu, 12 sun samu raunuka, sakamakon hatsarin mota a Kano

Sai dai ya shawarci mutanen da ke zaune a yankunan koguna da su daina tafiye-tafiye da daddare domin kogin Neja na iya mamaye gaɓarsa lokaci zuwa lokaci saboda ruwan sama mai ƙarfi.

Wani ganau ya shaida wa NAN cewa kwale-kwalen ya yi yunƙurin tsallakawa ƙauyen Mashayan Dundeje ne domin karɓar itace a lokacin da bala’in ya auku.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Okasanmi Ajayi, ya ce an tura jami’an rundunar zuwa wurin da lamarin ya faru domin ƙarfafa ayyukan ceto.

Ajayi ya ƙara da cewa ana kuma sa ran waɗanda aka aika za su gabatar da rahotonsu a hukumance.

1 COMMENT

Leave a Reply