No menu items!

Sample Page Title

Date:

A ranar asabar ɗin da ta gabata ne hukumar tsaro ta farin kaya ta SSS ta tabbatar da kama gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele da aka dakatar bayan an musanta shi da farko.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa sa’o’i bayan sanar da dakatar da Emeifele, an riƙa yaɗa rahotannin kama shi ta yanar gizo.

Sai dai kakakin hukumar SSS, Peter Afunanya ya musanta rahotannin. Sai dai a wata sanarwa a ranar Asabar, Afunanya ya tabbatar da kama gwamnan na CBN.

“Hukumar Tsaro ta Jihar ta tabbatar da cewa Godwin Emefiele, wanda aka dakatar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) yana hannun ta saboda wasu dalilai na bincike”.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta hana EFCC, ICPC, SSS tsare tsohon Gwamna Yari

“An umurci jama’a, musamman kafafen yaɗa labarai, da su yi taka-tsan-tsan a cikin rahoton da kuma labaran da suka shafi hakan,” Mista Afunanya ya rubuta.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...