Ɓarayi sun kai hari gidan yaɗa labarai, sun sace kayayyakin aiki a gidan rediyon Kogi

1
832

Wasu da ake kyautata zaton ɓarayi ne sun lalata kayan watsa labarai da wasu kayayyaki masu daraja a gidan rediyon jihar Kogi, da ke Ochaja.

An tattaro cewa an kai wa gidan rediyon jihar da ke Ochaja hari a daren ranar Litinin yayin da ɓarayin suka yi awon gaba da kayan watsa labarai da dama, haɗi da wasu kayayyaki masu daraja.

Jami’an ma’aikatar ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa, Mista Kingsley Fanwo da babban darakta na Hukumar Yaɗa Labarai ta Jihar Kogi, Alhaji. Ojo Oyila Ozovehe, ya kai ziyarar tantancewar kai tsaye gidan rediyon domin sanin irin ɓarnar da aka yi a tashar.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kai hari kan tawagar motocin gwamnan Kogi Yahaya Bello, da yawa sun jikkata

Sai dai Gwamna Alhaji Yahaya Bello ya umurci jami’an tsaro da su tabbatar da an kama waɗanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban ƙuliya domin daƙile aukuwar hakan nan gaba.

Kwamishinan ‘yan sandan, Mista Kingsley Fanwo a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce hukumomin tsaro na samun bayanan sirri masu amfani da za su taimaka wajen gudanar da bincike a yayin da ofishin ‘yan sanda na Egume ke aiki ba dare ba rana domin kamo waɗanda suka aikata laifin.

“Tare da irin ɓarnar da aka yi a tashar, abin takaici ne a lura da cewa Hukumar Kula da Watsa Labarai ba za ta iya yin aiki ba har yanzu.

Sai dai gwamnati ta duƙufa wajen maido da tashar ta iska da wuri “Yayin da muke gode wa Uban masarautar al’ummar da suka karɓi baƙuncinsa saboda damuwarsa kan wannan mummunan lamari.

Muna ƙira ga al’ummomin da ke da kayayyakin more rayuwa na gwamnati da su tabbatar da tsaron ababen more rayuwa saboda ɓarnar irin waɗannan kadarorin na rage saurin ci gaba.

1 COMMENT

Leave a Reply