No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnatin Jihar Kano na sanar da al’ummar Jihar cewa ba za ta lamunci auka wa gine-ginen mutane da sunan cin ganima ba, a dukkan sassan jihar.

Haka kuma gwamnati na bayyana takaicin ta bisa yadda wasu Matasa suka auka wa ginin dake cikin tsohon gidan jaridar Triump da ke Fagge alhalin wannan ginin baya cikin lissafin wuraren da za a rushe.

Saboda haka gwamnatin na ƙara jadadda cewar duk wanda aka samu da laifin auka wa wani gini tare da kwashe kayayyakin cikin sa zai gamu da fushin hukuma.

KU KUMA KARANTA: Ganduje ya sayar da dukkan motocin kwashe shara na gwamnatin Kano – Gwamna Abba

Gwamnatin ta ƙudiri aniyar yin aiki ne domin ci gaban Jihar Kano ba domin bai wa wasu lasisin rushe gine-gine da sace kayan mutane babu gaira babu dalili ba.

Wannan sanarwa ce da gargaɗi daga ofishin Sakataren Gwamnatin jihar Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...