Ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta Najeriya za ta shiga yajin aiki

2
330

Ƙungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta Najeriya ta ce za ta tsunduma yajin aiki sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

Ƙungiyar ta ce ta ɗauki matakin ne bayan da ƙungiyar ƙwadogo ta ƙasar NLC ta sanar da matakin tsunduma yajin aiki sakamon cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi, lamarin da ta ce ya haifar da ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.

Shugaban ƙungiyar mai lura da shiyyar birnin tarayya Abuja da Kogi, Godfrey Aba ya tabbatarwa da BBC cewa ƙungiyar za ta shiga yajin aikin daga ranar Laraba 7 ga watan Yuni, matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta janye matakin cire tallafin man ba.

Ya ƙara da cewa ”ƙungiyar za ta shiga yajin aikin ne har sai gwamnati ta janye matakin da ta ɗauka”.

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar mai ɗauke da sannun muƙaddashin sakataren ƙungiyar na ƙasar Dominic Igwebike, ta yi ƙira ga membobinta da su yi biyayya ga matakin ƙungiyar na tsunduma yajin aiki a tsakiyar makon da ke tafe.

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar NLC dai ta ce za ta fara yajin aiki tare da zanga-zanga daga ranar Laraba mai zuwa a wani mataki na nuna rashin amincewarta kan cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya, ta ba da umarnin yajin aikin gama gari ranar Laraba mai zuwa

Sabon Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ne ya sanar da matakin cire tallafin man fetur ɗin a cikin jawabin da ya gabatar cikin makon jiya a lokacin bikin rantar da shi.

Ita ma dai kungiyar ‘yan jarida ta ƙasar NUJ ta sanar da ɗaukar makamancin wannan mataki a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar.

2 COMMENTS

Leave a Reply