Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya ɗauki hayar motocin tifa domin kwashe shara a Kano, kamar yadda ake zargin magabacinsa, Abdullahi Ganduje, ya sayar da duk wasu motocin dakon shara na gwamnati.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Dawakin-Tofa, ya fitar, ta ce gwamnan ya amince da shirin kwashe shara na gaggawa na kwashe shara a kan titunan birnin Kano.
Gwamnan ya bayyana a matsayin abin takaici, yadda aka sayar da wasu muhimman kadarorin hukumar kula da tsaftar muhalli ta jihar, REMASAB, ga ‘yan uwa da abokanan tsohon gwamnan, “a ƙarƙashin wata rufa-rufa na wani kamfani mai zaman kansa na PPP, wanda hakan ya sanya aka yi hakan da wahala a cimma ingantaccen sarrafa shara”.
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kano ta kafa kotunan tafi da gidanka domin magance satar waya
“Sun sayar da dukkan muhimman kadarori da suka haɗa da manyan motoci mallakar REMASAB.
Ba mu da wani zaɓi da ya wuce ɗaukar hayar tipa da sauran kayan aiki da za a gaggauta kwashe juji daga tituna a wani yunƙuri na dawo da tsaftar muhalli mai inganci a Kano.
“Mun gano manyan wuraren da ake zubar da shara a cikin birnin don haka muka karkasa su zuwa shiyyoyi biyar domin fitar da su cikin inganci da za a fara nan ba da daɗewa ba. Za a gudanar da aikin ba dare ba rana har sai an tsaftace komai a Kano,” inji gwamnan.
Gwamnan, wanda ya nuna damuwarsa kan illolin da sharar tituna ke haifarwa, ya ce rashin halin ko in kula da gwamnatin da ta shuɗe ta yi game da tsaftar muhalli na iya haifar da asara marar misaltuwa a jihar, sakamakon ambaliya a damina idan ba a gaggauta kwashe manyan magudanan ruwa da shara suka toshe ba.
Idan dai za a iya tunawa, gwamnan ya amince da aikin Operation Nazafa, kwamitin yaƙi da zubar da shara, kwashe magudanar ruwa da tsaftace tituna wanda ya ƙunshi ƙungiyoyin masu ruwa da tsaki a jihar.
Gwamna Yusuf ya buƙaci mazauna Kano da su baiwa jami’an da za su gudanar da aikin kwashe shara haɗin kai, a cikin kwanaki masu zuwa domin kaucewa ambaliya, gurɓacewar yanayi da kuma illolin kiwon lafiya da ke da alaƙa da rashin tsaftar muhalli.
[…] KU KUMA KARANTA: Ganduje ya sayar da dukkan motocin kwashe shara na gwamnatin Kano – Gwamna Abba […]
[…] KU KUMA KARANTA: Ganduje ya sayar da dukkan motocin kwashe shara na gwamnatin Kano – Gwamna Abba […]
[…] KU KUMA KARANTA: Ganduje ya sayar da dukkan motocin kwashe shara na gwamnatin Kano – Gwamna Abba […]