Tsohon Gwamna El-Rufai ya zargi Buhari da sakaci wajen yaƙi da ta’addanci da ‘yan bindiga a Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya zargi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da gazawa wajen daƙile ayyukan ta’addanci, yana mai cewa tsohon shugaban ya yi watsi da shawarar da ya ba shi na shawo kan rikicin.

Ya yi wannan jawabi ne a yayin bikin rantsar da magajinsa, Sanata Uba Sani, a Kaduna, ranar Litinin.

El-Rufai ya ce: “A shekarar 2017, na roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ayyana ‘yan bindigar da suka kunno kai a matsayin ‘yan tayar da ƙayar baya, amma abin takaici, ba a yi haka ba sai 2022, bisa ga sanarwar da babbar kotun tarayya ta yi.

Abin takaici ne yadda Gwamnatin Tarayya ba ta yi la’akari da girman matsalar ba har sai da ‘yan bindigar suka yi ɓarnar rayuka, dukiyoyi, ’yanci da rayuwar mutane da dama.

KU KUMA KARANTA: Muna da ‘yancin mallakar muhalli don gudanar da rayuwarmu – Martanin almajiran Shaikh Zakzaky ga El-Rufai

“Duk da cewa an fara aikin soja tare da haɗin gwiwa a shekarar 2022, amma aikin bai cika ba.

Don haka, ina ƙira ga gwamnati da ta ci gaba da matsin lamba kan ‘yan bindiga, ‘yan tada kayar baya da ‘yan ta’adda, tare da sanya aikin soja ya zama cikakke kuma a lokaci guda a duk faɗin jihohi bakwai na gaba – shida a Arewa maso Yamma da Nijar – wadanda abin ya fi shafa.”

A martanin da El-Rufai ya mayar kan ƙalubalen da ya fuskanta a Kaduna, ya ce: “Gwamnatinmu ta yi aiki tuƙuru domin ganin ta daƙile ƙalubalen tsaro da ya kunno kai.

Matakan da muka ɗauka sun tabbatar da cewa ba mu samu wani rikici ba a faɗin jihar cikin shekaru takwas da suka gabata.”

A halin da ake ciki, sabon gwamnan ya yi ƙira da a samar da ‘yan sandan jihohi domin magance matsalar rashin tsaro a ƙasar.

Sani, a jawabinsa na farko, ya ce halin da ake ciki na buƙatar a sake duba dabarun. ya ce: “Jihar Kaduna ta samu kaso mai tsoka na zubar da jini da ɓarnar da ba dole ba.

Don haka, wannan gwamnatin za ta saka hannun jari sosai a duk wani yunƙuri da doka ta amince da su, gami da tura fasahar don tsaro da tabbatar da doka.

“Hakazalika, za mu taimaka wa ‘yan sanda, sojoji, jami’an tsaro da sauran hukumomin tsaro a jihar.

Har ila yau, za mu sa shugabannin gargajiya, cibiyoyin addini da shugabannin al’umma don tabbatar da ingantaccen tattara bayanan sirri, tare da yin aiki don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’ummomi daban-daban.


Comments

One response to “Tsohon Gwamna El-Rufai ya zargi Buhari da sakaci wajen yaƙi da ta’addanci da ‘yan bindiga a Najeriya”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Tsohon Gwamna El-Rufai ya zargi Buhari da sakaci wajen yaƙi da ta’addanci da ‘yan bindiga a Naj… […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *