Matawalle ya bar bashi mai tarin yawa a asusun jihar – Lawal Dare

0
906

Sabon gwamnan jihar Zamfara da aka rantsar, Dauda Lawal Dare, ya zargi tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle, da barin asusun jihar da basussuka masu ɗimbin yawa.

Lawal ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan an rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar a ranar Litinin.

Gwamnan, ya yi alƙawarin kawo ci gaba cikin sauri tare da magance ɗimbin ƙalubalen da ke fuskantar jihar.

“Ina so in sanar da jama’ar jihar cewa, asusun jihar babu ko kwabo, ya bar jihar da ɗimbin basussuka da suka kai biliyoyin nairori.

“Saboda haka, ina ƙira ga al’ummar jihar da su ƙara haƙuri tare da ba ni cikakken goyon baya da haɗin kai a wannan lokaci mai wahala.

KU KUMA KARANTA: An rantsar da Zulum, ya godewa al’ummar jihar Borno da suka sake zaɓensa a karo na biyu

“Na yi alƙawarin kawo ci gaba cikin sauri a jihar a lokacin yaƙin neman zaɓe, musamman ta fuskar tsaro, ilimi, samar da ayyukan yi, lafiya da kuma noma,” inji shi.

Lawal, wanda ya ce ya zo ne domin ceto jihar Zamfara, ya kuma yi ƙira ga matasa da su guji duk wani nau’i na miyagun ayyuka.

“Na zo ne domin ceto jihar Zamfara da yardar Allah kuma zan yi iya ƙoƙarina wajen ciyar da jihar gaba,” in ji gwamnan.

Tfohon gwamnan Matawalle da mataimakinsa Hassan Nasiha ba su halarci bikin rantsarwar ba.

Leave a Reply