An rantsar da Zulum, ya godewa al’ummar jihar Borno da suka sake zaɓensa a karo na biyu

2
1033

Gwamna Babagana Zulum na Borno da mataimakinsa Alhaji Umar Kadafur sun yi rantsuwar kama aiki a karo na biyu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa babban alƙalin jihar, Mai shari’a Kashim Zanna ne ya rantsar da su.

Da yake jawabi a wajen bikin, gwamnan ya godewa al’ummar Borno da suka zaɓe shi a karo na biyu.

Ya ce a lokacin mulkinsa na farko, gwamnatinsa ta aiwatar da ayyuka sama da 700, kuma yana fatan ƙara yin wasu ayyuka a wa’adi na biyu.

Zulum, wanda ya bayyana shirinsa na rangadin ƙananan hukumomi 27 na jihar, ya ce a yayin rangadin zai tattauna da masu ruwa da tsaki kan ayyukan da suka sa a gaba domin aiwatarwa a yankunansu.

KU KUMA KARANTA: Zulum ya ƙaddamar da rukunin gidaje 100 na na gwamnatin tarayya a Gwoza

Gwamnan ya bayyana farin cikinsa da dawowar zaman lafiya a Borno, inda ya ƙara da cewa ci gaban da aka samu ya kai ga komawa da kuma tsugunar da ‘yan gudun hijira sama da miliyan ɗaya a fadin jihar.

“Na tsaya a nan tare da mafi girman nauyin da ya rataya a wuyanku, mutanen jihar Borno.

“Na amince da wa’adin da aka ba mu na fara tafiya tare, wadda muke fatan za ta zamanto mai ɗorewa da kwanciyar hankali a karo na biyu na shekaru huɗu, insha Allahu.

“A gare ni, yi muku hidima, mutanen jihar Borno nagari sun kasance babban abin alfahari a rayuwata kuma ina ƙara jaddada hakan,” in ji shi.

Zulum ya yi alƙawarin cewa ba zai taɓa yin ƙasa a gwiwa ba wajen sauƙe nauyin da ya rataya a wuyansa ga al’ummar jihar.

2 COMMENTS

Leave a Reply