An rantsar da Mai Mala Buni a matsayin gwamnan Yobe karo na biyu

0
204

Daga Ibraheem El-Tafseer

A yau Litinin 29 ga watan Mayu 2023 aka rantsar da gwamnan Jihar Yobe Mai mala Buni a matsayin gwamna karo na biyu.

Buni wanda ya lashe zaɓen gwamna da aka yi a ranar 18 ga watan Maris, 2023 zai sake yin shekara huɗu kan karagar mulki bayan shekaru huɗu da ya riga ya yi daga shekaran 2019 zuwa 2023.

Gwamna Buni shi ne gwamnan jihar Yobe na huɗu da aka zaɓa bisa tafarkin dimokuraɗiyya, tare da yin alƙawarin cewa zai yi wa jihar hidima cikin mutunci da darajtawa.

Da yake jawabi a wajen rantsar da shi a birnin Damaturu ranar Litinin, Buni ya godewa al’ummar jihar kan yadda suka ga ya cancanta a sake zaɓensa a karo na biyu a kan karagar mulki.

“Haƙiƙa muna godiya sosai. Ina miƙa godiya ga kowa da kowa, bisa yadda kowa ya ba da nasa gudumawa wajen ci gaban jiha da ƙasa baki ɗaya.

“Abin da za mu yi da farko shi ne, mu ba da himma wajen ganin jihar Yobe ta samu zaman lafiya da ci gaba, ba tare da la’akari da wani bambanci ba,” inji shi.

Gwamnan ya bayyana cewa wa’adinsa na farko ya samu gagarumar nasara a fannin tsaro, kiwon lafiya, noma, kasuwanci, samar da ababen more rayuwa, gidajen jama’a, albarkatun ruwa, muhalli, mulki, albarkatun ma’adinai, bin doka da oda, sake fasalin ayyukan gwamnati da sauƙin kasuwanci.

Ya zayyana wasu nasarorin da aka samu da suka haɗa da: dawo da mutanen da Boko Haram ta raba da muhallansu, gyara dukkan makarantun da maharan suka lalata da kuma gyara da inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 138.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni ya rushe majalisar zartarwa ta jiha, ya kori kwamishinoninsa

Sauran, in ji shi, sun haɗa da kafa cibiyoyin raya dabbobi a gundumomin sanatoci uku, kammala kasuwannin zamani guda uku, gina gidaje 2,500 da kuma kafa dokar hana cin zarafin jama’a da dai sauransu.

Gwamnan ya jinjinawa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na musamman bisa ‘babban goyon bayan da yake baiwa jihar tare da yi masa fatan alheri a cikin ayyukansa na gaba.

“Shugaba Muhammadu Buhari, GCFR, Jagoran Talakawa, yana da matsayi na musamman a cikin zuciyata da kuma zukatan dukkan ‘yan Yobe. Muna godiya ga Allah Ta’ala da Ya ba shi ikon kammala wa’adinsa na shekaru takwas cikin kwanciyar hankali da lumana.

Gwamna Buni ya taya shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima murnar zaɓukan da suka yi da kuma rantsar da su, yana mai ba su tabbacin haɗin kan sa a gwamnatinsu.

“Shugaba Tinubu ya cancanci a zaɓe shi, fiye da kowane ‘yan takarar shugaban ƙasa, ganin cewa shi ne kan gaba wajen maido da dimokuraɗiyya a Najeriya.

“A madadin mutanen kirki na jihar Yobe, ina tabbatar masa da mataimakin shugaban ƙasa na jajircewa da goyon bayanmu kan babban aikin da ke gabanmu,” inji shi.

Leave a Reply