No menu items!

Sample Page Title

Date:

Tsohon shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya tashi zuwa filin taro na Eagle Square, inda za a gudanar da bikin rantsar da shugaban ƙasar, domin zuwa mahaifarsa ta Daura a jihar Katsina.

Buhari ya bar wurin ne da misalin ƙarfe 11:02 jim kaɗan bayan miƙa wa magajinsa, Bola Tinubu.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa babban jojin Najeriya, Kayode Ariwoola ne ya rantsar da Tinubu da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima.

Kafin ya shiga motarsa, an hangi Buhari yana ɗaga hannu ga magoya bayansa a wurin taron.

An tattaro cewa shugaban zai nufi filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, inda za a kai shi jihar Katsina.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya sha rantsuwa a matsayin shugaban ƙasar Najeriya

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...